Makirce-makircen shaidan

Mujallar Lafiya Jari Laifin Wa? Zauren Baki Awon mata masu ciki Baiwar Allah: 'Yan tagwaye Cutar hawan jini Cutar sarke hakora Cutar tarin fuka Daula ta kwarai Gudawa Hattara Dai Iyaye Jan hankali akan Bola Makirce-makircen shaidan ZIKIRIN ALLAH

Kadan daga cikin makirce-makircen shaidan

Mujallar Al-kibla (bol. 2, issue 4 – Ramadan 1425)

Fassara – Aminu Suleiman Jahun, 400L MBBS, BUK/AKTH.

 

A cikin hudubar ban-kwana, Manzon Allah (SAW) yace “Ku kiyayi shaidan domin kiyaye amincin addininku. Ya riga ya fidda rai cewa bazai taba iya batar da ku ba a manyan abubuwa, don haka ku kiyaye kada ku bishi a kananan abubuwa.”

 

Hakika shaidan akwai shi da dabara, naci, da kuma hakuri. Yana yaudarar mutane da son zuciya, camfi, da tsoratarwa na karya (K4:119). Manufar sa ita ce ya kautar da mutum daga hanyar gaskiya in yaso mutum ya kasance hasararre a ranar da za’a tara kowa domin sakamako. Sai dai kuma Manzon Allah (SAW) ya sanar damu cewa idan muka rike Al-Kurani da Sunnah, shaidan ba zai samu wani tasiri ba wajen kawar damu daga manyan shika-shikan addininmu. Don haka zai yi kokari yasa mubishi a kananan abubuwa ta hanyar tsare-tsarensa da shirye-shiryen manakisoshi a hankali kuma a bibiye har sai ya zamanto muna duban manya-manyan abubuwan kamar basu taka kara sun karya ba a wurin mu. Kuma tunda yana da ransa har izuwa tashin kiyama, yana da isasshen lokaci. Don haka Manzon tsira (SAW) yake mana gargadi akan wannan. A kokarinsu na jaddada wannan ne ma manyan malaman musulunci suke shawartar mutum musulmi da idan ya tashi duban zunubi, kada ya dubeshi a matsayin girmanshi ko kankantarshi, sai dai ya dube shi ta fuskar Wanda ake sabawa, wato Wanda ake karyawa dokar! – Allah Madaukakin Sarki.

 

Ali dan Abi dalibi ya bada wani labari da yake nuna makircin shaidan da yake shiryawa a hankali har ya rugurguza mana imani. Wannan labari akan wani mutum ne mai imani da yawan aiyukan addini, da yake zaune nesa da garinsu domin kuwa garin mamaye yake da alfasha. A cikin wannan garin akwai wasu mazaje su uku ‘yan uwan juna da suke kula da kanwarsu wadda ita ma babu ruwanta. Wata rana sai sukayi shawara su dauke ta su kaita can wajen gari inda wancan bawan-Allah yake zaune ko ta kubuta daga munanan dabi’un da suka mamaye garin. Daga farko wannan bawan-Allah ya ki don kuwa yasan hadarin kadaituwa da budurwar da ba matarsa ba. Amma sai nan da nan shaidan ya rada masa “kaga, kai ne mutumin da yafi kowa tsoron Allah a wannan waje. Idan kaki karbar wannan yarinya har ta koma wancan garin, lallai da sannu zata lalace.” Don haka sai ya karbe ta.

 

Da fari yana bar mata abinci a bakin kofar dakin ya tafi abinsa, sai shaidan ya dawo ya kuma rada masa cewa” ta yaya kasan cewa hakika tana samun abincin? Zai fi ka rinka dakatawa kadan kana tabbatar da cewa tana samun abincin ba wata dabbar bace ke cinyewa.” Saboda haka sai ya rinka tsayawa.

 

Bayan wani dan lokaci sai shaidan ya rada masa “kaga ga yarinya mai hazaka a kulle a gidan nan kai kuma gaka da irin wannan tarin ilimi. Ba zai fi ba ace ka fara koyar da ita in yaso zamanta anan baya zama hasara ba gaba daya?”. To daga nan fa sai ya fara koyar da ita darussa. Da farko yana barin wani abu a tsakaninsu saboda gudun fitina, amma sai shaidan ya bashi shawara a zuci cewa ya kamata ya rinka kallon idanunta yayin karatun domin ya tabbatar da cewa tana koyon, ba barci kawai take yi ba abinta.

 

Daga nan fa shaidan yasan cewa tarkon nasa ya danu. A hankali a hankali har sai da mutumin nan yayi wa yarinya ciki. Bayan hakan ya auku sai ya dawo ya rada masa cewa ”to fa kai ne mafi imani a garin nan. Yanzu ko mutuncin ka ya gama yawo (in har aka gano wannan katobara). Abin da yafi sai ka kashe ta ka binne, in yaso sai ka cewa ‘yan uwanta ‘rashin lafiya tayi, kuma duk da kokarin ka na neman magani sai da cutar ta kashe ta’. Wannan tabbas zai fi wancan abin kunyar”. Haka kuwa ya yi.

 

Da ‘yan uwanta suka zo duba ta, mutumin har da hawaye, yana basu labarin yadda cuta ta kamata, da irin kokarin da yayi na magani har ta mutu. Babu wata jayayya suka yarda, don kuwa kowa ya san shi mutumin kirki ne. A ranar da daddare duk su ukun sukayi mafarki cewa wannan mutumin ne ya kashe musu ‘yar uwa ya binne a wani wuri. Da safe sukayi ta mamaki da ta’ajabi ga yadda duk su ukun sukayi mafarki iri daya, sai suka yi shawara da su je wannan wuri da suka gani a mafarki su tone. Ai kuwa sai ga gawar yarinya har da juna biyu. Suka kamo wannan mutum suka tafi da shi cikin gari gaban jama’a. Mutane suna can suna shawarwarin yadda za’a yi da shi sai shaidan ya zo masa ya nemi mutumin da yayi masa sujjada inyaso shi kuma zai fitar da shi daga wannan bala’i. Da mutumin ya ga ba mafita sai ya yarda kuma ya aikata hakan (wal iyazu billahi). Daga nan shaidan ya bace ya rabu dashi – ya barshi a cikin masifa da halin da na sani.

 

Haka kuma wato shaidan bazai taba hakura ba har sai ya ga mutum ya cika. A lokacin da Imam Ahmadu dan Hanbali yana kan gadon mutuwa, mutanen da ke kusa dashi suka yi kokarin suyi masa magana, sai suka ji yana ta cewa “tukunna dai, tukunna dai.” Bayan ya farfado sai suka tambayeshi dalilin hakan. Sai yake gaya musu cewa a wannan lokacin yana ganin shaidan sarai a bisa garu yana ce masa “ya dan Hanbali, lallai imaninka mai karfi ne. Tabbas ka kubuta daga sharri na.” Shine shi kuma yake ce masa “tukunna dai”, don kuwa ya san cewa ko a lokacin, shaidan so yake ya sa masa jiji-da-kai da girman kai. Wato har a lokacin yana dana masa tarko ne. idan da a ce yaji shi wani ne daga cikin zababbu, to da Allah Ta’ala Ya haramta masa gidan al-jannah, don kuwa Manzon Allah (SAW) ya fadi cewa duk mai girman kai ko da dai-dai da kwayar zarra ne, aljannah ta haramta a gare shi.

 

A karshe, ya kamata mu sani cewa duk da irin wannan wayo da dabara ta shaidan, ba shi da wani tasiri a zukatan muminai. Allah Ta’ala Ya bamu damar zabi, wato muna da ikon zabi tsakanin halal ko haram, gaskiya ko karya, musulunci ko wani abu daban, kuma nauyin wannan zabi ya rataya a wuyan mu.