Jan hankali akan Bola
Jan hankali akan Bola
Sirajo Sulaiman Muhammad, 400L MBBS, BUK/AKTH, ssmuhammad@yahoo.com
GABATARWA
Babban dalilin da ya jawo hankali na wajen yin rubutu a game da Bola ya biyo bayan wata ziyara da wani abokina wanda yake daga daya daga cikin jihohin arewa ta gabas ya kawo min.
Mun kewaya da shi cikin garin Kano, don ziyarar ‘yan’uwa da kuma ganin muhimman abubuwan tarihi da manyan gine-gine da kuma uwa uba, kasuwannin dake wannan birni mai albarka. Mun shiga cikin unguwannin birnin nan yadda ya kamata a dan zaman da yayi lokacin wannan ziyara tasa.
Bayan mun gama zagayenmu muna hira sai yake cewa “Gaskiya, Kano tana da girma da kwarjini sai dai akawai Bola”. Wanna maganar ta girgiza ni kwarai da aniya. Ya ci gaba da nuna cewa bayan za kaga Bola a tsakiyar titi ta kare sauran gidaje dake kusa da ita, kai har ta zama wani abin kwatance wajen masu hawa motar haya da ma masu motar. Kaji yaron mota yana fadin “akwai na Bola” ko “daga bola ba zamu sake tsayawa ba”.
Abin takaici ne, ka ganta a ko ina; a bakin lungu, akan titi ko a tsakiyar titi, a cikin tsakiyar gidaje, a gefen asibitoci ko kuma a gefen makarantu ko a cikin kasuwanni. Ko a debo kwata a tara ta a barta ta bushe kai sai kayi zaton ba dan-adam ne yake giftawa ta wajen ba.
Samuwar bola dole ne saboda harkoki na yau da gobe sai dai yadda ake tafiyar da al’amarinta shine abin tsokaci a yanzu. Wani abin takaici shine yadda ake barin yara suke ta yin wasa akan bola. Wanna zai iya jawo wa su yaran ko kuma su dauki cutar da idan bata tafi dasu ba to kuwa zata wahalar da iyayensu.
Haka nan yadda zaka ga ana bawa yara su zubar da shara idan an debo ta daga cikin gidaje su zo su watsar da ita wani lokaci a kan hanya. Suje kuma ba dole su wanke hannuwansu ba su sayi dan-tamatsitsi ko kuma wainar fulawa da ake soyawa a nan kusa da bolar su ci.
TARA BOLA.
Bola tana taruwa ta hanyar zubar da abubuwa marasa mafani ko wadanda amfaninsu ya kare. Bola takan fito daga gurare da dama; gidaje, asibitoci, ma’aikatu, masana’antu ko kasuwanni. Haka nan takan hada da kashin dabbobi ko ma na mutane, saboda da yawa daga cikin yaran da ke unguwanninmu ko kuma almajirai zaka ga sun tafi kusa da bola sun tsuguna.
Yawancin sharar da akeyi a gidajenmu zaka ga an barta a wuri guda, kaji na barbazawa, maimakon da an share a debe. A inda kuwa ba’a samun gatan sharar sai kaga gidan sai kace bola. Bama irin dakin samarin mu wadanda ake yiwa lakabi da “an sanku ba’a san makwancinku ba.” A dakunan irin wadannan samarin ranar da za’a yi shara sai an bada sanarwa saboda duk wani mai abu mahimmi ya kau da shi, in an fita da ita kuwa kai ba kaga yawanta ba, amma ranar barci har da saleba.
ILLOLI.
A duk inda aka tara shara ko bola, to an samarwa kwari masu yada cuta wurin zama, sai suyi ta yaduwa. Nan da nan kaga beraye, kyankyasai, gafiyoyi da jaba sun yayyadu. Daga nan suma sai suyi ta yada cututtuka. Haka nan ita ma iska ta debi rabonta ta kai inda take so.
Wani abu da bola shine zaka ga yara a unguwanninmu suna ta wasa akai, nan da nan sai yaro yaji ciwo ko kwalba ta yanke shi, har wata kila ya samu cutar sarke hakora. Wani abin lura shine yadda ake saye da sayarwa na abubuwan ci a kusa da bola kamar su mangwaro, kayan miya da sauransu yadda nan da nan sai sai kaga cuta ta yadu. Kai ko babu komai, bola bata da dadin gani ballantana ka wuce ta kusa da ita, ai nan da nan wari ya daki hancinka.
SHAWARWARI.
Ina ganin a wannan gaba ya kamata na bawa bangarori daban-daban shawarwari wadanda nake ganin suna da ruwa da tsaki wajen magance wannan matsala. Da farkon fari, iyaye mata wadanda su suke tattara wannan shara daga gidaje, yana da kyau su samar da abin tara shara (dust bin) rufaffe wanda ba’a samu kudaje na hawa kai ba ko kuma iska take rabawa. Wannan zai taimaka kwarai wajen ganin an rage yaduwar cuta. Idan kuma za’a zubar da sharar a samu mutum mai hankali ba yaran da zasu dinga wasa da abin tara sharar kafin su dawo ba. Abinda ya kamace su shine a share gida kullum a tara sharar sannan a zubar.
A duk sanda aka fito da shara daga gidaje, ko ‘yan kasuwa suka fita da ita daga kasuwanni, ko ‘yan makaranta daga makarantarsu, kula da ita yana kan mutanen da suke kusa da wannan bola, da kuma gwamnati.
Samari da dattijan unguwa ya kamata su samarwa da bolar unguwarsu wajen da zai zamo yana da saukin matsala bisa la’akari da yanayin garin mu. Wannan shine mataki na farko da mutane zasu bi. Sai kuma ya kasance suna tunawa hukumar da take da alhakin kwashe sharar a kai-akai don debewa. Irin wadannan rukuni na mutane ya kamata su tsawatar wa yara idan suna wasa a kan bola ko kuma su hana saye-sayensu a wajen da wannan bola take don gudun kamuwa da cuta.
A bangaren gwamnati kuwa mun ga irin kokarin da tayi wajen kafa hukumar kula da shara da kuma diban ma’aikata. Bama haka ba, har da ci gaban da aka samu wajen debe sharar. Duk da haka muna rokon gwamnati da ta kara himma da azama, ta kuma kara kayan aiki ko gyara wadanda suka lalace, da karo ma’aikata; wannan zai kara taimakawa. Sannan zamu yi kira a gareta da ta sanya kwararru suyi nazari mai zurfi wajen ganin an samar da hanyar sarrafa sharar cikin sauki.
RUFEWA.
Tunda yake ya zama dole a tara bola saboda yadda ake amfani da abubuwa yau da kullum, to hakki ne akan kowa ya bayar da gudunmawar sa wajen ganin cewa bata zama wata hanya ba ta illa ga mutane don amfanin kawunan mu gaba daya. Wannan zai taimaka wajen ganin cewa garin ‘dalar gyada’ bai koma na ‘dalar bola’ ba.