Hattara Dai Iyaye

Mujallar Lafiya Jari Laifin Wa? Zauren Baki Awon mata masu ciki Baiwar Allah: 'Yan tagwaye Cutar hawan jini Cutar sarke hakora Cutar tarin fuka Daula ta kwarai Gudawa Hattara Dai Iyaye Jan hankali akan Bola Makirce-makircen shaidan ZIKIRIN ALLAH

Hattara Dai Iyaye!

Sani Abdullahi Tsoho.

500L MBBS, BUK/AKTH.

sanikura2006@yahoo.com.

 

Tarbiyya, ilimantarwa, hulda da mutane, da shige-da-ficen yaro na kadan daga cikin abubuwan da iyaye suke sa ido akai domin a samu manyan gobe nagartattu. Amma sai dai wani abin takaici shine mafiya yawan hadarurruwan dake faruwa a cikin gidaje yara yafi shafa. Wannan kuwa bazai rasa alaka da sakacin iyaye a wasu lokutan ba, kamar ajiye wasu kayan amfani yau  da kullum a inda yara zasu iya dauka, misali wuka, reza, matsefata, wuta, ruwan zafi, rude, miya mai zafi ko ma tuwo mai zafi, kalanzir, fiya-fiya, shinkafar bera, magunguna na uwa ko maigida ko na sauran yaran dake gidan, fadowa daga bene, ko gado mai tudu. Sauran sun hadar da cizon kunama, miciji da dai sauransu. Wadannan kan haifar da cuta, kai harma da nakasa ga yaranmu, alhali kuwa ana iya kare afkuwar wadannan hadarori.

 

KUNA

Na iya faruwa a kowanne sashe na jiki. Garwashi, ruwan zafi, rude da miya na kadan daga cikin abubuwan da zasu iya kawo kuna. A saboda haka, kiyayewa da gusar da wadannan abubuwa daga inda yara suke nada muhimmanci.

Idan kuma har ya faru, me za’ayi: -

·         A hanzarta cire kayan da ke jikin yaron.

·         A samu ruwa mai sanyi tsaftatacce a dinga zubawa a kan kunar.

·         Idan wurin na da girma sai a sami tawul, ko kyalle mai tsafta a rufe kunar sannan a hanzarta zuwa asibiti.

·         Kuna kan haifar da illoli da dama ajiki misali, karewar ruwan jiki, karancin jini, cutar zazzabi, ciwon fitsari, sarke hakora, canza kamanni, kagewar jijiyoyi,  ko kuma ma a rasa rai, a saboda haka iyaye sai ai hattara.

 

SHAN KALANZIR.

A kwai bukatar da zarar ya afku, a hanzarto zuwa asibiti. Baiwa yaro manja, ko madara,  a sanin ma’aikatan lafiya bashi da wani alfanu sai dai ma haifar da matsala, ga misali, madara ko manja zai iya shiga hanyar iska ya haifar da wahalar numfashi wanda zai iya sanadiyyar rasa rai. Bada maganin da zai sa yai amai shima matsala ne, a saboda haka, sai a kiyaye su; Hausawa dai sun ce ‘riga kafi yafi magani’.

 

KARSHE.

Kariya anan shine a nesanta duk abin da zai iya haifar da illa ga yaro daga duk inda zai iya dauka, a hana su tafiya ba takalmi, ko shiga ciyayi da surkukiya. Idan kuma har abinda ake gudu ya afku, babu bukatar jinkiri, a hanzarta neman lafiya daga kwararrun ma’aikatan lafiya, domin masu iya magana sunce ‘taya Allah kiwo yafi Allah Na nan’.