Gudawa

Mujallar Lafiya Jari Laifin Wa? Zauren Baki Awon mata masu ciki Baiwar Allah: 'Yan tagwaye Cutar hawan jini Cutar sarke hakora Cutar tarin fuka Daula ta kwarai Gudawa Hattara Dai Iyaye Jan hankali akan Bola Makirce-makircen shaidan ZIKIRIN ALLAH

GUDAWA: Rigakafin Kamuwa Da Ita Da Maganinta.

Balarabe Suleiman Amin,

500L MBBS, BUK/AKTH

 

Gudawa ita kadai ba cuta bace amma alamace da take nuna cewa wani abu yana tafiya ba dai-dai ba a jikin dan-adam. Gudawa itace mutum ya sami sauyin bayan gida (kashi) kamar karuwar yawansa (sau hudu ko fiye) a rana, canjin yanayinsa ba kamar yadda mutum ya saba yi ba. Bugu da kari, yana da matukar muhimmanci mugane cewa yara kanana musamman na goye sunfi manya nesa ba kusa ba shiga cikin hadarin kamuwa da gudawa, kuma yara sukan galabaita sosai fiye da manya a duk lokacin da sukayi gudawa musamman ma idan akayi rashin dace tazo da amai (hararwa).

 

Hanyoyin kare faruwar gudawa sun hada da:

 

·         Tsaftar muhalli. Ya kamata a tabbatar da tsaftar muhalli, kamar share gida da kewaye a kalla sau biyu a rana (safe da yamma)

·         Amfani da abin zuba shara rufaffe domin barin abin zuba shara a bude kan jawo kudaje da kadangaru gida, kuma yara sukansa hannuwansu a ciki domin daukar wani abun su yi wasa da shi.

·         Rufe masai da murfi a koda yaushe.

·         Nisantar da masai daga gurin dafa abinci, rijiya da sauransu.

·         Zubar da kashin yara a masai da zarar sun gama domin barinsa a bude a cikin gida kan jawo kudaje wadanda zasu dauki kwayoyin cuta daga kashin susa acikin abinci, ko rowan sha wanda wannan kan jawo gudawa.

·         Rufe randa da murfi wanda zai rufeta ruf, domin barinta a bude kan jawo fadawar kwayoyin cuta cikin ruwan.

·         Wanke hannu da sabulu ko kasa mai kyau bayan gama bayan gida (kashi).

·         Kulawa da tsaftar jiki da kayan sawa. Ya kamata a tabbatar da yin wanka kullum, sa tufafi masu tsafta, da yanke farce kafin yayi tsaho domin barin farce zako-zako kan jawo kwayoyin cuta su makale a karkashin farcen wanda wannan kan haifar da gudawa.

·         Wanke kayan dafa abinci da sabulu da kuma ruwa mai kyau kamarsu tukunya, kwanuka, wukake, ludaya, da dai sauransu, kafin amfani dasu.

·         Yin amfani da tsaftataccen ruwa domin sha da dafa abinci. Idan kuma ana da kokwanton ingancin ruwan, ya kamata a tafasashi, a kuma barshi ya kwanta kafin amfani da shi.

·         Tabbatar da nunar abinci kafin aci, domin cin abincin da bai dahu sosaiba kan haifar da gudawa.

·         Rufe tukunya da murfi yayin dafa abinci.

·         Amfani da kwanuka masu tsafta domin cin abinci.

·         Abincin da aka dafa ya dade ko ya kwana ya kamata a dumama shi sosai kafin aci. Kuma kada aci abincin daya fara lalacewa koda an dumama.

·         Wanke kayan lambu da ruwa mai kyau ko kuma ruwan gishiri kafin amfani dasu.

 

Ga wanda ya kamu da gudawa ya kamata a bashi taimakon gaggawa a gida kafin a kaishi asibiti, ta hanyar a bashi ruwan gishiri da sukari akai-akai har zuwa asibiti [a auna sukari karamin cokali (na shan shayi) goma, gishiri cokali daya a hada da ruwa mai kyau kwalabar lemo biyu, ko a tafasa ruwa ledar fiya-wata (wato pure water) daya]. Yara na goye masu gudawa dole ne a lokacin da sukeyi a kara lokacin da ake basu domin tsotson nono.

 

Alamomin galabaita ga mai gudawa sune:

  • Fita daga hayyaci
  • Faduwar madiga a yara
  • Fadawar idanu
  • Bushewar baki
  • Da dai sauransu

 

A asibitine za’a iya gano abinda ya kawo gudawar domin maganinsa, kuma maganin da za’a bayar ya danganta da abin da likita ya gano (wato abinda ya kawo cutar). Daga karshe ina cewa alura ‘Taya Allah kiwo yafi Allah Nanan’.