Daula ta kwarai
DAULA TA KWARAI (1): Labarin Zuciya Da Jiki.
M.M. Abubakar Ringim
500L MBBS, BUK/AKTH
Nan bada jimawa ba, a Hindu, anyi wani yaro mai suna Yakzan, sunan tsohon sa Yanam, kakansa kuwa Yabsir. Yaron yana da lura, gashi kuma da kwazo. Tun kuruciya yayi karatun Muhammadiyya, gashi kuma an sashi boko. Tsohonsa ko baiyi karatu kwarai ba. Kakan ko dattijo ne mai nazarin al’amuran duniya. Lokaci-lokaci yaron kan je suyi tadi. Kullum kuma ya dawo makaranta sai ya fada tsohon da tambayoyin abubuwan da ya ji masu wahalar ganewa, gogan kuwa in ya gagara fahimta sai yace “kai rabani da surutun wofi, kul na kara ji ko in sabar ma. Haba! Yaro da tambaya sai kace dan nasara”. Shi kuwa sai ya kyale ya dangana. Wata rana suka yi darasi a makaranta kan kimiyyar jikin mutum sai ya nufi gida ya iske kakan kishingide a inuwa, ya tsuguna ya gaisheshi sannan yace “kaka menene rai? Me ke sa numfashi? Me ke sa zuciya bugawa? Menene garkuwan jiki?, yaya mutum ke tunani?” Kakan yayi shiru, can yace hala malam ya baku darasi kila dai baku fahimce shi ba, amma da ka tambaye shi aji da ka sami karin bayani. To daga yau ka rika tambayar malam ga duk batutuwa masu tsanani gareka, da haka watarana ina ga ka zama mashahurin malami”. Yaron ya ce “To”.
Allah sarki, fata na gari lamiri. Yanzu Yakzan ya zama malami duk ga boko da Muhammadiyya. Shine ma ya bamu wannan labarin da ke tafe game da zaman jikin bil-adama lokacin da muka iske shi gida, sai yayi bismillah ya ce:
“Shi jikin mutum zaune yake tamkar wata daula wadda Allah ya tsara zamanta, ga dai shugaba duk wato zuciya, ga kuma saraki wato kwakwalwa, ga soja da ‘yan doka masu kare garkuwan jiki, ga duba-gari su huhu da koda masu kula da tsabta, ga baitulmali su hanta da tsoka da kitse, harma ga sauran talakawan gari su hanji da ma sauran sassan jiki. Tun da Allah ya halicci jiki haka tilas sai ya azawa zuciya shugabanci kuma ga mataimakiya wato kwakwalwa domin jagoranci na kwarai da mulkin adalci nagari, kuma saura ya aza musu biyayya ga wadannan muddin ba’a keta shari’a ba kuma ba’a danne hakki ba. Ta haka jiki ke zaune cikin aminci saboda hadin kai, kowa na bada tasa gudunmawa, shugabanni ba zalunci ko hassada, talakawa kuma ba raini ko lalaci. Da ace wani sashe guda zai gagara cika aikin sa to da duk jiki sai ya kamu da rashin lafiya.
“To, na gaya muku zuciya ita ce shugabar jiki tunda nan ne mutum ke fara tunanin aikata abu, hairi ko sharri, kafin ma kwakwalwa tayi aniya, to yaya zuciya ke cika aikin ta? Domin wannan amsa, kuma don mahilicci ya nunawa mutane hikimar sa, sai wata rana sahabbai na tare da Manzon Allah (SAW) suka yi tambaya “shin da menene zasu ciyar don sadaka da kyautar tadawwu’i” alhali a lokacin kuwa ba’ayi hijira ba, sai aya ta sauka cewa da “afwu” wato sauran da ya rage bayan bukatar iyalinsu da wadanda ciyar dasu ya rataya ga wuyan su. (duba kuma bayanin surar Al-bakara aya ta 215 da 219). Kuma Manzo (SAW) ya kara gaya musu cewa a jikin mutum akwai gaba guda, idan ta gyaru to jiki ya tsira don zai rika aikata hairan, amma idan ta baci to wannan ya halaka don zai yawaita zunubi, sai ya ce ai itace zuciya.
“Dalili kuwa an fahimci cewa zuciya ke buga jini tsarkakakke wanda ta amsa daga huhu dauke da sinadaran abinci da iska mai amfani ga jiki (odygen) zuwa ga dukkan sassan jiki har da kwakwalwa kanta, amma kafin nan sai ta shayar da kanta tukuna ta hanyar masinjojinta wato wasu jijiyoyin jini na musamman da suke isar mata da nata rabon. Koda ya ke itace taskar rabon abinci a jiki, zuciya bata da hadamar boye wani kashi don tanadin gobe kuma ba ta hassadar rabon sauran talakawan ta, hasali ma ta dogara ne ga baitulmali yayin bukata. Wannan kuma ya nuna mana cewa babu amfani mutum ya bar iyalinsa cikin bukata alhali yana bushasha a waje. Har yau dai zuciya ita ke amsar jini maras kyau mai dauke da iska maras amfani ga jiki (carbon diodide) daga duk sassan jiki ta buga shi zuwa ga huhu domin tsarkakewa da iska mai kyau ta numfashi, da kuma koda domin tace gubar jini a matsayin bawali”
Koda malam Yakzan ya kawo nan sai muka ji aljamiri na cewa “Allah ya baku mu samu”. Na yi farat nace “Allah cishe mu”. Malam kuwa sai yace “kila a ciki ba’a rasa wani abinci da aka gama bukata ba”. Almajiri yayi tsaye, na tashi na shiga na kawo gidauniya da sauran abinci gaba gareshi, ya juye ya tashi. Bayan nan malam ya ci gaba: “To, dazu na ce muku jiki na da baitulmali don adana sauran abinci saboda lokacin fatara ko bukata, sune su hanta da tsoka da ma kitse. In da rarar abinci sai su cika, in ko babu sai su motse. Haba! Baku lura kosasshen mutum sai ku ganshi bul-bul yana sheki, amma mai yunwa a jika sai ku ganshi duk a bushe? To ita hanta ke fara amsar sinadaran da ke cikin abinci wanda jini ya kawo don ta gyara ta raba su gida-gida, mai kyau ayi amfani da shi nan take inda bukata ko a adana don gaba, guba kuwa a ware ta don kar ta cuci jiki. Shi yasa hanta ke fara tabuwa in mutum ya sha guba, kuma takan ji wuyar aiki in an faye ciye-ciye barkatai, don haka Allah ya tsara mana lokutan cin abinci da hutu da azumi ko hanta ma ta dan samu sarari, sai ku kiyaye. Amma hanta na da jimiri ainun don ko an yanka ta gida uku kashi guda na iya yin aikin, saura kuma sai ta warke kamar da. Koda ma da juriya take. Don haka karamar cuta bata yi masu illa, amma da sun galabaita to nan fa jiki sai rashin lafiya, kila sai mutuwa. Akan yi dashe inda hali. Akwai matsar-mama kuma jikin hanta, tana fidda ruwan sinadari mai taimakon hanta don narka kitse da kuma cire guba daga jiki. Saifa kuma nata sinadarin yafi amfani wurin abinci mai sukar, kenan jinyar ta na iya kawo ciwon suga.
“Nayi muku batun sinadaran abinci, to tumbi shine ke fara amsar zallan abinci wanda aka hadiye, kuma shi tamkar fatar buhu ne, wato sai ya cika da abinci ko ya lafe idan babu. Yana da sinadarin asid da ke taimakawa wajen narka abinci ruwa-ruwa don ya bi zuwa ‘ya’yan hanji, su kuwa dogon bututu ne guda, a nade har uwar hanji. Suna iya tsotson ruwa-ruwan abincin nan mai cike da sinadaran gina jiki su tura zuwa ga hanta. Dussar abincin ko sai ta wuce zuwa dubura a kasaye ta.
“Bari mu duba batun sojoji da ‘yandoka, su nasu namijin aiki ne ja, don suke kare garkuwar jiki daga karyewa musamman idan kwayoyin cuta mahara sun kawo hari. Su soja na fitowa ne daga bargo kamar sauran ‘ya’yan jini. Yawansu ba misali domin kuwa ga su nan birjik suna yawo cikin jini, wasu ko na zaune suna jiran ko-ta-kwana a sassan jiki daban-daban. Don haka jiki kullum cikin tsaro yake, haka kuma Allah ke nunawa mutane su kiyaye, (ku duba kuma bayanin surar Al-imran aya ta 200 da Nisa’i aya ta 71). To, daga wani dan hari ya kawo kai sukayi arba da soja sai a shaya daga! Su sojoji kuma na da kan-gado, muddin sunyi yaki da wasu irin mahara sau daya tak suka ci nasara kansu to zasu fahimce su su kuma kiyaye da su ta hanyar wata alama don ko gaba zasu kuskura su kawo wani hari sai a shaida su take a gama da su cikin sauki, don anyi musu kwanton bauna tuni! Wannan ilimi Ubangiji ya fahimtar da mutum don haka yanzu akwai allurar rigakafin cuce-cuce musamman annoba, wanda ba komai bace face kwayoyin irin wannan cuta ne amma aka cire gubar su, wato dai wadannan maharan ne yanzu aka amshe kayan yakinsu aka gama su da sojan jiki a fahimce su don gaba.
“To, don tsananin aiki sojojin basu faye tsawon rai ba. Duk ‘yan satuttuka ne sai su mutu, wasu ko a fagen fama suke halaka. In kayi kurji har yayi diwa wanna cike take da gawarwakin soja da mahara, duba gari suka turo waje. To shi wanna yaki kullum ana yinsa alhali mu bamu da labari don kwayoyin cuta mahara na nan birjik cikin iskar da muke shaka da ruwan da muke sha da abubuwan da muke kamawa, kila sai sojojin sun galabaita ko mahara sun kusa cin gari kana mutum ya kwanta bayada lafiya, nan kuma tilas sai likita ya duba. Anan kuma ina son na ce muku fatar jiki itama wata babbar garkuwa ce dake hana miyagun kwayoyin cuta shiga jiki sa’annan kuma tana yin aikin dubagari don fidda guba daga jiki a matsayin jibi (gumi), kuma ta tare kura. Maganin wannan sai wanka da sabulu akai-akai. Ya kamata kuma ku sani ba duk kwayoyin cuta suke miyagu ba, a’a akwai na kwarai a cikin su. Sune ma ke taimakon mu kashe miyagun, wasu na taimako wajen narka wasu nau’in abinci a ciki kuma su bamu wani nau’in sinadari mai amfani a jika. Wadannan su abokanmu ne Allah Ya hada mu da su, muna basu mazauni da abinci su ko su na taimakon mu a wasu al’amuran na rayuwa, wato cude ni in cude ka!
“Har yau dai ga wani babban abun fadi game da kwayar cuta; Wata sa’a wasu dangogi na rikida su badda kama har soja su gagara shaida su don su bijirewa garkuwan jiki su mamayi jiki har suyi illa ainun. Yayin nan kuma jiki baya da katabus, ta haka ko wasu mahara kananan alhaki ma sai su kawo hari su ci gari. Kullum kuma jiki sai mashashshara, da ciwo iri-iri, ba sauki. Kai har abu ya gagara kila kuma sai mutuwa. Misalin irin wadannan miyagun kwayoyin cuta sune masu kawo cutar kanjamau. Har yau kuwa ba’a sami kwakkwarar makama ba, kullum ana bidar hanyar rigakafi amma saboda saurin rikidan nan sai a rasa wacce za’a kama, don ko yau anyi guda da an jima ta zama wofi. Sai dai yanzu akwai ‘yan kwayoyin magani masu rage aibin ciwon har ya jima bai buwayi jiki ba. Babban rigakafi a yanzu dai shine kame kai, don babbar hanyar kamuwa da ciwon shine yawan jima’i barkatai.
“Tsaya, na ambaci batun kwakwalwa daga karshe don ita ta gama aikin kowane sashen jiki. In kun tuna na ce muku ita saraki ce bata son abun da ya taba ta, dalili kuwa Allah ya halicce ta da raunin jure wahala. Zuciya da sauran talakawa ma duk suna sane da wannan, don haka a wasu lokutan tsananin bukata ma har suna yarda a kara mata rabon abinci daga nasu kaso! Kunji zaman daula ta kwarai inda ake mulkin adalci da gaskiya. Ga kuma wani abun mamaki, wato duk da raunin kwakwalwa haka amma ita tafi duk saura daukar tasku mai wuya. Misali, ita ke gudanar da tsarin mulkin jiki, ba da umarni ko hani, yin tsinkayen al’amura da basira, jin kararrakin talakawa da kuma yanke hukunci ko tsawatarwa. Wato ita kuma ce alkalin jiki. Tabbas iko sai Allah Mahalicci Mai hikima!
“To, kwakwalwa na da masinjojinta barkatai gwanayen isar da sako cikin gaggawa, sune jijiyoyin aikewa da sakwanni. Akwai su da dama cikin jiki, wasu kai tsaye suke isa gareta kamar daga ido don gani, da kunne don ji, da hanci don shaka, da harshe don dandano, wasu kuma sai sun biya ta laka kana su isa, misali daga kwankwaso don bayangida da bawali ko jima’i, da kafafu don tafiya ko gudu, dama hannaye don aikace-aikace. Huhu ko da zuciya da ‘yan hanji suna da duk irin masinjojin biyu. To, ko yaya dai duk ga kwakwalwa suka nufa su labarta rahoton halin da ake ciki, shin sanyi ko zafi, zaki ko daci, kamshi ko wari, dadi ko ciwo, aminci ko tsoro da sauran su. Ita ko sai ta duba matsalar tayi tsinkaye bisa kana ta aike da amsar umarnin da ya fi dacewa don a zartas da shi can.
“Misali idan kana zaune da dare sai kunne yaji motsi, nan take kwakwalwa zata samu labari sai ta aiki hannu “lalibi ashana, kunna fitila”, sai ido yace “ashe bera ne, sai ta aikawa jiki aminci kowa ya huta. Amma da ace ido yace “ai maciji ne!” Nan kam sai ta ce “jiki yi shirin gudu, kafa ruga duk a tsere”. To haka kuma idan abu na da kamshi sai a soshi, mai wari ko a guje shi. Ko kuma abinci mai zaki da mai daci. Kai! Lallai Allah yayiwa mutum arziki, ba don kwakwalwa ba da jiki kowa ya aikata abun da ya ga dama ba doka ba tsari kamar yadda zaman birni in ba shugaba da doka sai ya lalace. Watakila ciki zai ce akawo abinci, baki yace zai huta. ‘Yan doka suce a kama mahara, sojoji su ce a sake su. Kafar dama tace ayi gudu, ta hagu ta ce a tsaya, to ai da jiki ya gagara zama lafiya kenan”.
Da malam yayi shiru sai na ce “Gafarta, ashe kenan nan duniya muna iya shirya zaman dauloli bisa mulkin adalci muddin muka yi nazari da kwaikwayon zaman jiki da mulkinsa, kuma al’umma su zauna lafiya da juna misalin yadda jiki ke zaune lafiya?” Malam yace “I, ba shakka. Allah ai baya halittar banza, ko da tsiro ne balle dabba akwai misalai ababen lura da amfani ciki sai dai hankalin mutane ya kasa rabewa da su. Duniya ko yau ba gaskiya ne, don dai kun lura cewa mulkin jiki ba na kama karya ba ne, kuma ba daula ake ci da tsinke ba. Saidai zama ne na aiki tukuru da neman shawara da taimakon juna, wato wanke-ni-in-wanke-ka. Tsakanin shugabanni da talakawa kowa na da hannu cikin zartas da wani hukunci. Muddin ko haka ya dore to rayuwa ta mika kenan har abada. To, amma don Allah Ya cika alkawarinSa sai ya sanya ajali ga rayuwa. Ko da yake jiki na zaune lafiya, ana nan wata rana muddar zamaninsa zata cika sai tsufa ya kama wata gaba har ta galabaita. Shikenan jiki kuma sai illa, sai mutuwa. Ko kuwa ma ba ciwo ba tsufa sai tsautsayi ya afku kamar hadarin mota ko gobara. Wani ko ma ba ciwon, ba hadarin, ba tsufan, sai dai mutuwa kwatsam! To, amma dai duk a mutuwa zaka iske wani sashen jiki ne ya harbu har ya gagara cika aikinsa kamar da, musamman zuciya shu’umar aba ce: yanzu tana aiki, yanzu ta tsaya don wani dalili. A’aha, wata sa’a a asibiti bakuji ana cewa a duba gawa don a gano me ke sanadin mutuwarta, musamman idan ana neman shaidar shari’a domin wanda ake tuhuma a kotu?” Mukace “I”, yace “To ai duk musulmi yayi imanin Allah Ke rayawa da kashewa, amma hakika ga kowace mutuwa akwai sanadi, sai dai galibin lokaci yin duban ba zai canza alkiblar halin da ake ciki ba, yayin nan ko yinsa bai da wani karin fa’ida”.
Koda ya kawo nan sai aka zo aka kira shi ciki. Zamu tashi nace ‘Gafarta malam, lokaci na gaba ma ci gaba da wani sabon darasi”. Yace “To, Allah ya bamu lafiya”.