Cutar tarin fuka
Cutar tarin fuka na daukar sabon salo!
Dr. Anas Isma'il, Sashen Lafiya, Karamar Hukumar Enugu Ta Arewa, Enugu, Nigeria. ibnmalikanas@yahoo.co.uk
GABATARWA
Cutar Tarin Fuka (TB, wato tuberculosis) ta dade tana addabar bil-Adama. An san wannan ciwo tun kafin a sami magungunan kashe kwayoyin cuta (wato antibiotics). Bilhasali, babban masanin likitanci (Hippocrates) yayi bayani a kanta kimanin shekaru dari hudu da sittin kafin haihuwar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata agareshi). Akasari, ciwon na yaduwa ne ta cikin iska idan mai dauke da cutar yayi tari ko atishawa. Ciwon yana haddasa tari, fitar da majina da jini da matsananciyar rama; sanadiyyar tsamarin wannan ciwo, miliyoyin mutane ne suke rasa rayukansu.
Gano hanyoyin tabbatar da kasancewar cutar a jikin dan-Adam da magungunanta na daga cikin muhimman cigaba da masana harkar lafiya suka samu a shekarun da suka gabata. Babban abun damuwa da ke kunno kai a yanzu shine mummunan koma baya da aka samu game da wannan cuta kimanin shekaru ashirin zuwa talatin; wannan ya faru saboda kwayoyinTB marasa jin magani (resistant strains), yaduwar cutar fiye da kima saboda bullowar cutar kanjamau, hade da karuwar hayayyafar kwayoyin TB zuwa bangarorin jiki da ba’a saba ganin ta ba (wato edtra pulmonary tuberculosis) kamar kwakwalwa, zuciya, koda da sauransu. Wannan shine bahaushe ke cewa “bara mun yi wake bana mun yi harawa!”
Wannan koma bayanne ya sa masana, hukumomi, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar lafiya suka dukufa wajen samo bakin zaren. Amma har ya zuwa yanzu, nasarar da aka samu bata taka kara ta karya ba. Abin da ya kamata a sa a gaba shine kara himma wajen kare kai daga wannan cuta da taimakawa wadanda suka kamu da ita. Yin haka zai taimaka kwarai da gaske wajen maida wannan gagarumin kalubalen ya zama tarihi.
GIRMAN MATSALAR CUTAR TB
Kamar shekara ashirin da biyar baya, ana ganin akwai cigaba a yaki da cutar TB. Amma bayan bayyanar cutar kanjamau a farkon shekarun alif da dari tara da tamanin ne, hannun agogo ya fara komawa baya. Kiyasin da hukumar lafiya ta duniya tayi ya nuna cewa tun daga bayyanar cutar TB, mutane kusan biliyan biyu ne suka kamu da ita. Kimanin miliyan uku sukan rasa rayukansu a duk shekara sababin wannan cutar. An kuma tabbatar cewa TB ce a kan gaba wajen sanadiyyar rasa rayukan masu dauke da ciwon kanjamau. Ahalin yanzu, fiye da kashi tamanin bisa dari na wadanda ke iya yada cutar na kasashe masu tasowa (Afirka da Asiya). Wannan na kawo mummunan tarnaki wa cigaban tattalin arzikin wadannan kasashe saboda akasarin masu dauke da cutar matasa ne majiya karfi. Binciken ya kuma nuna cewa kamar kashi ashirin zuwa talatin bisa dari na al’ummar duniya ne ke dauke da kwayar TB. Bugu da kari, marasa lafiya da ke dauke da kwayoyin TB marasa jin magani da kuma masu ciwon kanjamau kullum kara yawa suke, kuma sun fi sauran masu dauke da cutar ta TB saurin hallaka.
YADDA CUTAR KE BAYYANA
Wata halayya da kwayar TB ke da ita shine dadewa a jiki (satuttuka ko watanni) kafin bayyanar alamominta. Kuma ko ta wane bangare na dan-Adam ta shiga, ta kansa zazzabi da yawan gumi da daddare, rashin cin abinci, rama, da kaluluwa. Ahalin yanzu, kusanba bangaren jikin dan-Adam da TB ba ta iya shafa; Idan ta shafi huhu, ta kan sa tari (mai fidda majina da jini), zazzabi, ciwon kirji, rama da rashin cin abinci.
Idan kuma kwakwalwa ta shiga, ta kan sa ciwon kai mai tsanani, amai, gushewar hankali; in ta yi tsamari, maras lafiya ya kan suma ko ma ya rasa ransa (an fi samun wannan a cikin kananan yara ko masu ciwon kanjamau). Kashin baya shine kwayar TB ta fi addaba idan kashi ta shafa; hakan yakan kawo ciwon baya ko shanyewar kafafu. Ta kan kuma iya shafar gabobi, musamman ma kwankwaso da gwiwa. Cutar TB kan haddasa ciwo a kwibi (idan koda ta kamu), mara, ko wajen fitsari. Idan mahaifa ko gaban namiji ya kamu, ta kan haddasa matsalar rashin haihuwa. Duka wadannan akan iya tabbatar da su ta hanyar gwaje-gwaje da kuma bincike a cikin jini, kakin majina, fitsari, hotunan sassan jiki daban-daban da likitoci kan bukata (kamar su radiographs da scans), da sauransu. A zamani irin na yau da cutar kanjamau (wato HIB infection) ta zama ruwan dare game duniya, a kan yi gwajin cutar kanjamau ga akasarin wadanda ke da cutar TB, domin bincike ya nuna cewa fiye da rabin wadanda ke da cutar kanjamau na dauke da cutar TB a lokaci guda.
KALUBALEN DA A KE FUSKANTA WAJEN KULA DA MASU CUTAR TB
i. Alakar Cutar TB Da Kanjamau
· Cutar kanjamau na matukar raunata garkuwar jiki, [musamman ma fararen kwayoyin jini masu yaki da kwayar TB (wato CD4+ cells)], wannan ya sa masu cutar cikin hadarin saurin kamuwa da TB da sauran cututtuka masu yaduwa, (wato infectious diseases) da kuma saurin hayayyafar kwayoyinta da bazuwar su zuwa sauran sassan jiki.
· Karfin garkuwar jikin masu kanjamau (musamman yawan CD4+ cells) shi yake nuna yawan cutar TB a jikinsu.
· TB na taimakawa saurin hayayyafar kwayar kanjamau (wato HIB) zuwa matakin da cutar ke bayyana a fili (wato AIDS).
· Cutar TB na da wahalar tabbatarwa (ta fuskar bincike) da wahalar magani idan akwai ciwon kanjamau.
· Cutar TB ce sanadiyyar rasuwar akasarin masu dauke da cutar kanjamau
ii. Matsalolin Da Ake Fuskanta Wajen Maganin TB
Manya-manyan matsalolin dake fuskantar ma’aikatan lafiya wajen maganin cutar TB na da yawa. Muhimmai daga ciki sun hada da:
· Watanni (ko ma shekara) da ake shafewa ana shan magani na sa marasa lafiya su gaji, wasu ma su yi watsi da shan maganin gaba daya. Wannan na daga cikin dalilan da ke sa kwayar TB bijirewa magani (drug resistance), wanda kuma ke jawo maida hannun agogo baya; ta yadda sai ta kai ga amfani da wasu magunguna sabbi (wato second line drugs), wadanda ke da matukar tsada da kuma matsaloli irin nasu (wato side effects). Saboda haka ne masana suka kawo shirin ‘sa ido akan shan magani’, (Wanda ake kira ‘directly obserbed therapy’, wato DOT).
· Abubuwan da magungunan TB ke haddasawa (wato side effects). Misali, sukan yiwa hanta ko koda lahani; kwayar Rifampicin (daya daga cikin magungunan TB) na sa jan fitsari.
· Karancin magungunan ainihi da kuma matsalar jabun magungunan (wadda ta zama ruwan dare a Najeriya) na yin matukar barazana ga nasarar maganin TB. Ko da yake magungunan ya kamata ace kyauta a ke rabasu ga masu bukata, a Najeria, matsalolin tattalin arziki na kan gaba wajen kawo ci baya wajen aiwatar da wannan!
iii. Rukunan Masu TB Da Ke Bukatar Kulawa Ta Musamman
- Mata masu ciki:
Ana iya shigar da gwajin cutar TB cikin gwaje-gwajen da a ke yi wa mata masu ciki domin gano wadanda za su amfana da magani. Daukan hoton D-ray ne kawai likitoci ke muhawara a kan hadarinsa ga abin da ke cikin mace (musamman a wata uku na farko). Amma idan likita ya ga cutar ta kama mai ciki da karfi, yakan fifita yin hoton D-ray a kan rashin yinsa.
Domin rage matsalolin da maganin ke iya haifarwa (wato side effects) ga uwa da jaririnta, akan jinkirta bada maganin TB zuwa wani lokaci. Amma idan likita ya fahimci cewa rayuwar uwa na fuskantar barazana, akan fara magani ba tare da wani jinkiri ba. Likitoci da yawa na da ra’ayin cewa uwa ta cigaba da shayarwa alhalin tana shan maganin TB.
- Kananan yara
Yara ba sa yada cutar TB ga yara ‘yan uwansu. Sukan dauki cutar ne daga manya. Yaran (musamman kasa da shekara biyar) da TB ta jawo masu ciwon sankarau (wato tuberculous meningitis) na shiga cikin mawuyacin hali (fiye da manya) da yakan kai ga rasa rai. Abin ban sha’awa shine, yara daga shekara biyar zuwa goma sha biyar ba safai suke kamuwa da TB ba.
- Masu dauke da ciwon kanjamau
Karfin garkuwar jikinsu (da ake aunawa ta yawan CD4+ cells), halin da hantarsu da kodarsu suke ciki da kuma tsananin cututtukan guda biyu ne ake amfani da su don sanin wane magani za’a bayar [na kanjamau (wato ARBs), ko na TB (wato anti tuberculous drugs), ko kuma a hada su gaba daya]. Hakan ya zama wajibi ne saboda akasarin magungunan kanjamau da na TB na iya yiwa hanta lahani ko kuma su rage karfin junansu (kamar tsakanin Rifampicin da Efibarenz). Amma hukumar lafiya ta duniya (World Health Organization) ta bada shawarar kammala maganin TB kafin fara na kanjamau; sai dai inda aka ga kanjamau din na barazana ga rayuwar maras lafiya.
Idan likita yaga cututtukan guda biyu na neman kai maras lafiya kasa, yakan bada magungunan gaba daya lokaci guda. Abin da ke da matukar muhimmanci a nan shine karfafa gwiwar marasa lafiya su daure da shan magani; saboda magungunan na da yawa kuma wasunsu ba su da dadin dandano ko kuma sukan sa haraswa (amai).
INA MAFITA?
Nauyi ya rataya akan masana, hukumomi (na gwamnati da masu zaman kansu) da al’umma gaba daya wajen maganin wannan babbar barazana da ke fuskantar al’ummar duniya.
Masana su samar da shugabanci, su kuma kara bada himma wajen bincike da wayar da kan jama’a, su ja hankalin hukumomi su yi abin da ya kamata; su kuma sa ido sosai wajen kula da masu kanjamau, musamman ma wadanda ke dauke da cutar TB. Gwamnatoci su taimakawa masana, ta samar da magunguna da alluran rigakafi. Kamfanoni da kungiyoyi masu zaman kansu su tallafawa musu wajen bincike da shirya tarurrukan masana wajen samo sabbin hanyoyin tunkarar wannan matsala.
Ban da ba da kyakkyawar kulawa ga marasa lafiya, gudanar da bincike nauyi ne da ya rataya a kan cibiyoyin lafiya domin su samar da bayanai na kididdigar masu cutar, masu shan magani da sauransu. Wannan ne zai sa a fahimci irin cigaban da a ke samu ko akasin haka; zai kuma bada dama a yi gyara a guraren da ya kamata domin samun sakamakon da a ke bukata. Iyaye su tabbatar an yi wa ‘ya’yansu allurar rigakafi ta BCG domin bincike ya tabbatar tana bada kariya daga cutar TB mai tsanani. Yana da kyau iyalan masu dauke da TB su je asibiti a binciki lafiyar su, su kuma taimaki marasa lafiyar, su kara musu karfin gwiwa wajen shan magani don a sami nasarar da ake bukata wajen rage wannan ciwo. Yin hakan zai taimaka kwarai da gaske (hade da wasu hanyoyin masu yawa da wannan fage ba zai iya bayani a kansu ba) wajen rage girman wannan matsala da ta zamar wa bil-Adama alakakai.
GODIYA
Babban likita, masanin cututtuka masu yaduwa, Dr. Abdurrazak Garba Habib ya taimaka wajen rubuta wannan kasida. Allah ya saka masa da alkhairi, Amin.