Cutar sarke hakora

Mujallar Lafiya Jari Laifin Wa? Zauren Baki Awon mata masu ciki Baiwar Allah: 'Yan tagwaye Cutar hawan jini Cutar sarke hakora Cutar tarin fuka Daula ta kwarai Gudawa Hattara Dai Iyaye Jan hankali akan Bola Makirce-makircen shaidan ZIKIRIN ALLAH

Cutar sarke hakora ta jarirai 'yan kasa da kwana ashirin da takwas

Rubutawa: Maimuna Abdulkarim Halliru, 500L MBBS, BUK/AKTH, maimunahalliru@yahoo.com

Fassara: Muhammad Sabiu Aliyu, 400L MBBS, BUK/AKTH.

Cutar sarke hakora tana daya daga cikin cututtukan da kan iya yaduwa a tsakanin mutane, wato wani kan dauka daga wani. Koda yake cuta ce dadaddiya tun kaka da kakanni, duk da haka har yanzu akwai karancin fahimtar yanayin wannan cuta cikin wannan al’umma. Wanda hakan ya haifar da yawan faruwar cutar da kuma mace-mace a tsakanin yara manyan gobe, sakamakon kamuwa da wannan cuta.

Cutar takan auku farad-daya sakamakon gurbatar rauni da kwayar cutar wadda takan rayu a cikin kasa, bayan gidan dabbobi (kashin dabbobi) da na mutane, da kuma sauran gurbatattun abubuwa.

HANYAR YADUWAR CUTAR.

Cutar sarke hakora ta jirajirai ‘yan kasa da kwana ashirin da takwas takan faru ne yayin yanke cibi, shaushawa, balli-balli, da kaciya wadanda aka yi da aska ko abin yanka gurbatacce.

Hakazalika akan kamu da cutar sakamakon shafar wani gurbataccen abu (tsumma da makamantansu) ga cibiyar da aka yanke ko sabuwar kaciya. Amfani da wadannan abubuwa yakan bambanta daga wata al’umma zuwa wata, kuma sun hada da:

·          Kashin dabbobi;

·          Toka;

·          Tsimin itatuwa;

·          Dadai sauransu.

ALAMOMIN BAYYANAR CUTAR.

Cutar sarke hakora takan dau kimanin rana daya zuwa wata biyu tsakanin shigar kwayar cutar jiki zuwa lokacin baiyanar alamomin kamuwa da ita. Alamar farko itace kin kama mama ga jarirai. Sauran alamomin sun hada da sarkafewar hakora da sankarewar jiki da kuma rikewar tsokokin jiki gaba daya, akai akai.

MAGANI.

Koda yake akwai magunguna daban-daban da akan yi amfani dasu wajen magance wannan cuta, babban magani shine rigakafi. Wannan gaskiya ne, ai dama masu hikima sunce rigakafi yafi magani. Domin kuwa idan yaro ya kamu da wannan cuta maganin kan taimaka ne kawai domin kare tabarbarewar yanayin cutar. Haka ne ma yasa gaggauta kai jaririn da ya fara nuna alamun cutar asibiti ya zamanto yana da matukar muhimmanci a matakin farko na magance cutar.

KARIYA.

Matakan kariya su sukafi sauki, arha, da kuma tabbas sama da magance cutar bayan kamuwa da ita. Matakan kariya su ne:

·          Tabbatar da ingantacciyar tsafta lokacin haihuwa da kuma tabbatar da tsafta da kyakkyawan yanayi ga mai nakuda sa’annan ayi amfani da reza ko aska mai tsafta, mara kura ko dauda wajen yanke cibiyar jarirai. Wannan zai samu ne ta hanyar bawa unguwarzomomi horo na musamman tare da yi musu bita da kuma ziyararsu a wuraren aikinsu akai-akai. Kari akan haka shine a tabbatar da an wanke cibiyar da ruwan wuta (wato spirit) bayan an yanke domin kare ribanyar kwayar cutar. Dadin dadawa, wanzamai su tabbatar da sun gasa askarsu sa’annan su wanke ta da ruwan wuta (wato spirit) kafin kaciya, shaushawa, balli-balli da sauransu.

·          Mataki na biyu shine yin allurer rigakafin cutar ga mace mai ciki. Don haka yana da matukar muhimmanci da zarar mace ta samu ciki ta hanzarta zuwa bangaren renon ciki a asibiti don karin bayani game da rigakafin wannan cuta da sauran cututtuka.

MARUFI.

Cigaba da yawan faruwar wannan cuta a cikin al’umma ‘yar manuniya ce da kai tsaye take nuna sakacin hukumar Lafiya da iyaye a cikin wannan al’umma saboda dalilai kamar haka:

·          Rigakafin wannan cuta yana da sauki wajen bawa yara, baya tattare da wata illa, ga araha da kuma inganci.

·          Yin burus da nuna halin ko inkula ga wannan cuta mai kisa da kuma sa jinya matsananciya ill ace babba wajen rage rigakafi ga mata da yara kanana. Tabbas babu raba daya biyu mun dau hanyar halaka ‘ya’yanmu da kanmu, idan har bamu yi hattara mun gyara halayyarmu ba game da wannan cuta.