ZIKIRIN ALLAH
ZIKIRIN ALLAH
Ibrahim Salisu
500L MBBS, BUK/AKTH
barhams2000@yahoo.com
Zababbun, dadadan, tsarkakakkun gaisuwa sun tabbata ga Allah daYa halliccemu, Yayi mana baiwa da addinin musulunci, Ya samu cikin al’ummar fiyayyen, zabebben, babban masoyin Allah, Annabi Muhammadu (SAW). Allah Kayi ruwan tsira mai yawa ga masoyinKa, dan lelenKa kuma shugaban manzanninKa Annabi (SAW), da mutanen gidansa da sahabbansa da masu bin tafarkinsa har zuwa ranar karshe.
Saboda mutukar dimaucewa da musulumai suka yi, musamman a wannan lokaci namu na karshen zamani, game da kai kawo wajen neman duniya da yawan shagaltuwa da ita, yasa naga yakamata mu fadakar da kawunan mu game da wasu daga cikin falalolin ambaton Allah (SWT) wadanda zasu taimaka mana a wajen cika ma’auninmu na lada cikin sauki ba tare da wahala ba.
MA’ANAR ZIKIRI
Zikirin Allah na nufin duk wani abu da dan-adam zai yi na ibada wanda zai sa shi cikin tunanin Ubangiji Mahaliccin sa. Ya kunshi zikirin Allah da harshe da zuciya, karatun kur’ani, salatin girman Allah da ikonSa, da mulkinSa da halittunSa da sauransu. Sai dai a wannan makala za’a fi bada karfi da zikirin Allah da ya shafi harshe.
FALALAR ZIKIRI
Akwai ayoyin Alkur’ani mai girma da kuma hadisai na Manzon tsira masu yawa dake bayani game da falalar zikirin Allah. Amma in Allah Ya yarda za’a ambaci kadan daga cikin su ne kawai:
· Allah Madaukakin Sarki Yayi alkawarin bayar da aljanna ga masu yawaita ambatonsa daga cikin maza ko mata. (Suratul Ahzabi).
· Allah (SWT) Yana umartar mu da mu yawaita ambatonSa domin mu samu rabauta da rahamarSa (Suratul Jumu’ah).
· An karbo hadisi daga Abdullahi dan Busrin, yace wani mutum ya ce “ya ma’aikin Allah, lallai shari’o’in musulunci sun yi yawa a gareni, ka bani labarin wani abu da zanyi riko dashi”. Sai Annabi yace masa, “kada harshenka ya gushe yana danye, wato yana mai laushi saboda ambaton Allah” (Tirmizi).
· Manzon Allah ya tambayi sahabbai, “yanzu dayanku zai gajiya wajen samun lada dubu kowane yini?”. Daya daga cikin sahabbai yayi mamaki ya tambayi Annabi, “ta yaya?” Sai yace masu “mutumin da yace Subhanallahi sau dari, sai a rubuta masa lada dubu ko a shafe zunubansa dubu” (Muslimu).
· Duk sanda mutum yace Subhanallahi Wa Bihamdihi, za’a dasa masa itace na dabino cikin aljanna (Tirmizi).
· An samo hadisi daga Abu Sa’id (R.A) yace Manzon Allah (SAW) yace “wasu mutane basu taba taruwa ba suna ambaton Allah (SWT), face mala’iku sun kewaye su, rahamar Allah ta lullube su, natsuwa ta sauka a garesu, kuma Allah Zai ambace su ga mala’iku da suke tare daShi” (Muslimu).
· Annabi Muhammadu (SAW) yace “akwai wasu kalmomi guda biyu, masu saukin fada ga harshe, masu nauyaya ma’aunin lada, ababen soyuwa ga Allah Mai rahama; kalmomin sune mutum ya rika fadin “Subhanallahi wabihamdihi, Subhanallahil azimi” (Bukhari da Muslimu).
· Zikirin safe da yamma - wasu daga cikin zikirori, Annabi ya kwadaitar damu game da fadar su musamman safe da rana, a kowace rana. Suna kunshe da falala mai girma. Misali Abu Huraira yace Annabi Muhammadu (SAW) yace, “Duk wanda yace ‘La’ilaha illallahu wahadahu lasharika lahu, lahul mulku, walahul hamdu wa huwa ala kulli shai’in kadeer’ a cikin yini sau dari, zai samu lada kwatankwacin wanda ya ‘yanta bayi goma, kuma za’a rubuta masa lada dari, za’a kankare masa laifuffukansa dari, kuma zai samu kariya daga shaidan na wannan yini dukkansa, sannan kuma babu wanda zai zo da ladan da yayi nashi a ranar kiyama sai dai wanda ya karanta wannan zikiri da adadin da yafi nasa” (Bukhari da Muslimu). Allah Madaukakin Sarki Ya umarce mu da mu rika ambatonsa muna gode masa, kuma muna tsarkake Shi safe da yamma (Suratul Gafir). Abu Huraira ya karbo hadisi daga manzon Allah (SAW) a inda yake cewa “Duk wanda yace, Subhanallahi Wabihamdihi sau dari safe da yamma to babu wani da zai zo da lada kwatankwacin na sa sai dai wanda ya fada kamar yadda ya fada ko kuma ya dada bisa adadin da ya fada (Muslim). Abdullahi ibn Khubaib yace “Manzon Allah ya umarce ni da na rika karanta wannan surori; kulhuwallahu, da suratul falaki, da suratun nasi, kowacce sau uku kullum, safe da yamma domin zasu isar mani daga kowane abu” (Abu Dawun da Tirmizi).
Sayyidina Usman, Allah ya yarda dashi, yace Manzon Allah (SAW) yace “Babu wani bawa da zai rika fadin wannan zikiri safe da yamma, sau uku face Allah ya tsare shi daga dukkan sharri watau; Bismillahillazi la yadhurru ma’a ismihi shai’un fil ardhi wala fissama’i wa huwassami’ul alimu” (Abu Dawud da Tirmizi).
· Zikirorin bayan sallar farilla - Manzon Allah ya kasance da ya gama salla yana yin istigfari wato fadar “Astagfirullah” sau uku, sannan yace “Allahumma antassalamu, waminkassalamu, tabarakta ya zal jalali wal ikrami” (Muslim).
· Mu’azu Ibn Jabal yace wata rana Annabi ya rike hannuna, yace “Mu’azu, wallahi lallai ina sonka”. Kana yace “zanyi maka wasiyya da kada ka bari, bayan ka gama kowace salla, fadar - Alhumma a’inni ala zikrika, wa shukrika, wa husni ibadatika” Abu Dawud.
· Annabi Muhammadu (SAW) yace “Duk wanda yake cewa ‘Subhanallahi, walhamdulillahi wallahu akbar’ kowacce sau talatin da uku sannan ya cika ta dari da fadar ‘la’ilaha illallahu wahadhu lasharika lahu, lahul mulku walahul hamdu, wahuwa ala kulli shai’in kadir’, za’a gafarta masa dukkanin kananan laifuffukansa koda sun kai yawan kumfar kogi” (Muslim).
YANAYI KO LOKUTAN ZIKIRI
A kowane lokaci ko hali mutum zai iya ambaton Allah; ko a tsaye ko a zaune, ko a kwance, ko lokutan tafiya ko mutum baya da alwalla, ko lokacin janaba, ko lokacin haila (al’ada ta mata), lokacin da mace take da jinin biki. Allah (SWT) Ya bayyana cewa bayinSa masu cikakken tsantsar hankali sune masu ambatonsa a halin tsayuwa, a zaune ko a kwance…”(Suratul Ali’imrana).
Nana A’isha tayi bayani cewa Manzon Allah (SAW) yana ambaton Allah a kowane yanayi yake ciki (Muslimu). Shi yasa ma yake umartarmu koda lokacin da mutum zai sadu da iyalinsa sai yace “Bissimillahi Allahumma Jannibnasshaidana wa jannibisshaidana ma razaktana”. Idan Allah ya kaddara samun dan da, to Allah zai kiyaye shi daga sharrin shaidan (Bukhari da Muslimu).
Haka kuma ya umarce mu lokacin shiga ban-daki da muce “Allahumma inni a’uzhu bika minal khubusi walkaba’isi”. Bayan an fito kuma sai ace “Gufranaka, Alhamdu lillahil lazi azhaba annil aza wa’afana.
LADUBBAN ZIKIRI.
Ana bukatar mai ambaton Allah ya zama mai tsarkin niyya, kuma da tsoron Allah, da halarto ma zuciyarsa abinda bakinsa ke fada, da kasancewa cikin tufafi da wuri mai tsafta idan zai yiwu, da kuma rashin cutar da ‘yan uwansa ta hanyar zikirin da yake yi.
“Kuma ka ambaci Ubangijin ka cikin ranka da kaskantar da kai, da tsoro, da koma bayan bayyanawa na magana, da safe da maraice. Kuma kada ka kasance daga cikin rafkanannu (Shagalallun mutane)” (Suratul A’araf).
LAZIMTAR ZIKIRI.
An fi so mutum ya zama idan ya kama wani daga zikirin Allah, to ya dauwama yana yi, kada yayi fashi. Wannan kwadaitarwa ce daga Allah da manzonSa; “…. Kuma ayyuka masu kyau wadanda aka dauwama wajen aikatawa sun fi yawan lada ga Ubangijinka…”
Haka kuma Nana A’isha ta karbo hadisi daga Annabi Muhammad (SAW) inda yake cewa “Mafi soyuwa a ayyuka na addini a wajen Allah shine wanda mai aikata shi ya dauwama akansa” (Bukhari da Muslim). Shi yasa Annabi ya umarci sahabinsa da kada ya bari wani lokaci ya wuce baya ambaton Allah da harshensa kamar yadda ya gabata a can baya.
KAMMALAWA
Mun gode Allah (SWT) da ya bamu wannan kyauta ta hanyar yin biyayya gareshi da kuma yawaita ambatonSa. Kada mu bata lokutan mu na rayuwa a shagale-shagalen duniya wadanda baza su karar damu da komai ba sai hasara da nadama. Lallai zikirin Allah ibada ce mai girma, mai sauki, ba tare da wahala ba, sannan kuma ga yawan lada wanda zai nauyaya ma’auni na aiki domin samun rahamar Allah ta Aljanna a gobe kiyama. Allah ya karba mana dukkan ibadoji, ya bamu ikon biyayya gare shi, ya kiyaye mu daga sharrin shaidan, ya gafarta mana dukkan laifuffukan mu. Allah ka gafarta ma iyayenmu, ka yi masu kyauta da jannatul firdausi amin summa amin.