Baiwar Allah: 'Yan tagwaye

Mujallar Lafiya Jari Laifin Wa? Zauren Baki Awon mata masu ciki Baiwar Allah: 'Yan tagwaye Cutar hawan jini Cutar sarke hakora Cutar tarin fuka Daula ta kwarai Gudawa Hattara Dai Iyaye Jan hankali akan Bola Makirce-makircen shaidan ZIKIRIN ALLAH

Bayani akan haihuwar 'yan biyu.

M.M. Abubakar Ringim, 500L MBBS, BUK/AKTH, dwinfos@hotmail.com

 “Yan biyu kyautar Allah”, haka Hausawa ke fadi idan an sami karuwar da ‘ya’ya biyu suka fito maimakon guda da aka saba gani. Batun iya haihuwa kuwa baiwa ne domin ba kowa ke da ikon ba. Haka dai Allah Ta’ala Yace (ku duba bayanin surar shura Aya ta 49 da 50). Wannan kuma don adalcin Sa ne, kana iske wasu na haihuwar maza zallansu, wasu ko sai mata, wasu kuma ga maza duk game da matan.  Haka kuma wasu na neman haihuwa idanu rufe amma Allah bai nufa ba. Sai kuma wasu na haihuwa biyu-biyu ko fiye da haka duk lokacin da suka sami juna biyu. Hakanan idan ya nufa sai kaga wasu tagwayen sun fito jikinsu hade da juna, sai dai wannan  ba’a fiye samun irin su ba. Binciken kimiyya ya nuna cewa  bakar fatar Afirka sun zarta sauran al’ummar duniya wajen haihuwar tagwaye, shima yafi ga kabilun yarbawan Najeriya musamman ‘yan Ilesha, don duk haihuwa dubu a sami tagwaye har 50 ciki maimakon 12 a Turai ko 5 rak can kasashen gabas. Kuma tagwaye masu kamanni ban-ban sun fi yawa ga masu kamanni guda.

Mace na iya gadon haihuwar tagwaye, kuma ana danganta shi da samun juna biyu yayin manyance, ko yawaita samun juna biyu, ko ma yin amfani da maganin sa haihuwa. To bari mu duba me ke faruwa har asamu shigar ciki: Da fari galibi lokacin jima’i akan yi dace da inzali, to sai ‘ya’yan maniyyin namiji suyi ta ninkaya suna tsere zuwa ga kwai na matar, shi kuwa yana fita ne wata-wata daga daya daga cikin jakankunan kwai guda biyu da mace ke dasu gefen mahaifarta, guda a dama gudan a hagu. Lokaci daya kuma ita mahaifar na can tana shirya sheka don tsammanin zuwan dan-tayi ko da ciki zai shiga, idan ko bai shiga ba to wannan sheka sai ta wargaje, sababin  jinin al’adar mace kenan. To idan an dace ga kwai guda ya fita kana ga dan maniyyi guda ya iso sai su gamu Allah Ya nufi ciki ya shiga kenan. Shike nan, wannan jaririn ciki, wanda yake kamar kwai, sai ya dawo cikin mahaifa ya shiga sheka ya fara girma don nan gaba kadan sai ya zama dan-tayi, matar kuwa tana ta hidimomin ta bata ko ankara ba tukun, (duba kuma surar A’araf aya ta 189).

To yaya tagwayen ke faruwa? Haka ne, wata sa’a sai ka iske kwan jaririn ciki saboda wani dalili ya rabu subul gida biyu ko fiye tun da wuri-wuri kafin ya girma zuwa dan-tayi, to wannan ke faruwar tagwaye masu jinsi guda (maza ko mata) kuma masu kamanni guda don asalin kwansu guda ne. Wata sa’a kuma matar ke fitar da kwai biyu to fiye lokaci guda kuma duk cikinsu ya shiga da maniyyi daban-daban, don haka sai a samu tagwaye masu jinsi ban-ban (mace da namiji) ko kuwa jinsi guda amma kamanni ban-ban don asalin su ba guda bane. Kunji ban-bancin su. Idan kuma kwan jaririn ciki ya tashi rabuwa amma yayi latti har dan-tayi ya kusa girma to sai ya gagara ida rabuwa kuma ya zauna haka rabi-da-rabi. Wannan shike faruwar tagwaye masu jiki guda da kai biyu, Ajab! Ko kuwa ka gansu kowa da jikinsa amma gasu damfare da juna, su kuma iri-iri ne: Ga masu haduwa ta kai kila har kwakwalwar su hade take, ga wasu ta gadon baya har ta yiwu su hada laka, wasu ko ta kirji har ka iske juciyarsu guda ce ko kuwa sun hada kayan ciki. Kai, wasuma fatar jiki kurum suka hada, wadannan da sauki kenan.

To, a tadin diyan tagwaye dole na fadi cewa shi samun cikinsu yana kara hadarin irin matsalar da akan samu a juna biyu tun daga laulayin ciki zuwa su karancin jini a jika da matsalar nakuda da haihuwa, kamar galabaitar jarirai, makalewar jarirai, zubar jini, matsalar shayarwa, da ma mutuwa in da karar kwana. Don haka ya kamata mai juna biyu ta fara awo da wuri kuma ta ci gaba akai-akai don a rika duba ta da jaririn kuma ta rika amsar shawarwari.

Akwai masu ganin wai tagwaye na rikida zuwa maciji ko kunama, to kila dai aljanu ke wa mutane gizo don anyi camfi. Ga addini kambun baka gaskiya ne sai dai ba’a kebe shi ga tagwaye bisa hususiyyar su kadai ba. Amma game da tagwaye a hade da juna ko masu kai biyu, wadannan wasu zasu ce aljanu ne, to na dai gaya muku dalilinsu. Kuma irin su da an zo ga likita zai duba ya ba da shawarar matakin da za’a dauka. Galibi su kan rayu har girma ba tare da an raba su ba. Akwai wasu a Turai har suka yi aure suka hayayyafa, kuma suna yin wasan kwallo ma! Idan matsalar ta shafi zuciya ko kwakwalwa ne to ba dama a raba su ba tare da guda ya tabu ba, ko ya mutu, ko a rasa su duk. Kwanan baya wasu likitoci sun raba irin wadannan a wani asibiti a Badun, Najeriya, amma suka mutu daga baya. Sai dai idan matsalar ba mai tsanani bace misali wadda ta shafi fatar jiki, ko kuma akwai bukatar a ceto jariri guda, to nan kam babu laifi a yi tiyata ko da gudan zai rasu, wannan ko sai an shirya da gaske.