Awon mata masu ciki
Bayani akan awon mata masu juna biyu.
Sani Abdullahi Tsoho, 500L MBBS, BUK/AKTH, sanikura2006@yahoo.com
Awon ciki wata dabi’a ce ta zuwa wajen likita ga mata masu juna biyu domin duba lafiyar su da kuma jaririn dake cikin su, domin samun lafiyayyiyar uwa da kuma jariri mai lafiya, da koshi, gami da kuzari.
MANUFAR AWO
· Domin gano wata matsala ko larura da zata iya shafar uwa yayin da take da ciki.
· Domin gano larurar da zata iya nakasar da jaririn dake cikin cikin-mahaifiya.
· Domin gano kiyasin lokacin da uwa zata haihu.
AMFANIN AWO
· Awo na da amfani masu yawa ga uwa da abin da ke cikin cikinta, domin yana taimakawa wurin raguwar mace-macen mata da jariran su wurin haihuwa, da kuma bayan an haihu.
· Awo na taimakawa wajen gano cututtukan da kan addabi iyaye, kuma su haifar da matsala da cikin da suke dauke da shi, misali zazzabin cizon sauro, karancin jini, ciwon sukari, hawan jini, amosanin jini, cikin tagwaye, da dai sauransu.
· Fadakarwa domin cin abinci mai gina jiki kamar hatsi, shinkafa, wake, doya, kifi, nama, madara, kwai, da kuma kayan lambu da ganyayyaki (kamar su alaiyahu, kuka, zogale, lemo, abarba, goba, mangwaro, da dai sauran su), domin jariri yana cine daga abinda uwa taci.
· Sanar da masu juna biyu irin canje-canjen da zasu samu ajikin su, kamar kumallo, kasala, wadanda basu wuce misali ba.
· Karantarwa domin sanin muhimmacin shayar da nonon uwa ga jariri.
· Sanar da su alamomin matsala ga mai ciki, kamar ciwon kai mai tsanani, jiri, gani dishi-dishi, ballewar jini, da daina jin motsin yaro, domin a hanzarta zuwa asibiti.
YADDA AKE ZUWA AWO
Dazarar an sami ciki, akwai bukatar zuwa awo kamar haka:
I. Sau daya duk bayan sati hudu har ciki ya kai wata bakwai
II. Sau daya duk bayan sati biyu har zuwa wata takwas da rabi
III. Duk sati bayan wata takwas da rabi har zuwa haihuwa
Amma ga masu matsala, ko masu bukatar kulawa ta mussamman kamar mata masu ciwan sukari, hawan jini, cikin tagwaye, da dai sauran su, sukan je awo kamar haka:
I. Duk bayan sati biyu har zuwa wata bakwai
II. Duk sati bayan wata bakwai har zuwa haihihuwa
DUBA MAI CIKI DUK LOKACIN AWO
· Duk zuwa akan auna nauyin mai ciki, a gani shin ko yana karuwa kamar yadda ya kamata ko a’a domin a dauki matakin daya dace.
· Girman cikin shima ana auna shi, domin yawan girmansa ko kankantarsa suna yin nuni daban-daban.
· Bugun jinin uwa ana duba shi domin a tabbatar daidai yake.
· Ana duba nimfashin yaron, domin a san halin da yake ciki.
· A kan dauki jini domin a gano yawan jinin uwa.
· Ana yin gwaji na fitsari a lokacin awo.
BADA MAGANI
Duk zuwa awo, a karshe bayan likita ya gama duba mai juna biyu akwai magunguna da ake rubutawa wadanda ke taimakawa wurin samun isasshen jini, da kuma na bada kariya daga zazzabin cizon sauro domin uwa ta dinga sha har haihuwa.
A karshe muna fatan magidanta zasu kara bada himma wurin zaburar da iyalin su wurin halartar awo domin muhimmancin sa wurin lura da lafiyar uwa da jaririn da ke cikin-cikin, kuma idon haihuwa ta zo a taho asibiti.