Mujallar Lafiya Jari

Mujallar Lafiya Jari Laifin Wa? Zauren Baki Awon mata masu ciki Baiwar Allah: 'Yan tagwaye Cutar hawan jini Cutar sarke hakora Cutar tarin fuka Daula ta kwarai Gudawa Hattara Dai Iyaye Jan hankali akan Bola Makirce-makircen shaidan ZIKIRIN ALLAH

Rigakafi ya fi magani!

Barka da zuwa wannan shafi na mujallar lafiya jari. Zagaya ka duba rubuce-rubuce iri-iri da muka wallafa a daba'o'in da suka shude na wannan mujalla. Idan kana da wata shawara ko tambaya, sai ka tuntubemu ta adireshinmu.

Daga teburin Edita.

Alhamdulillahi, wassalatu wassalamu ala rasulillahi, wa ala alihi wa sahbihi, wa man tabi’ahum bi ihsanin ila yaumuddin. Assalamu Alaikum wa rahmatullah.

 

Hakika dukkan yabo ya tabbata ga Allah da Ya bamu ikon kammala wannan daba’i na mujallar Lafiya Jari. A wannan karon ma mujallar na kunshe da kayatattun rubuce-rubuce masu dimbin amfani da ilmantarwa. A koda yaushe rubuce-rubucen mujallar suna bada muhimmanci ne ga rigakafi, domin duk kankantar ciwo lafiya tafi shi, kuma duk kyan magani gwamma karma a sami cutar.

 

A ciki zaku ji irin yadda cutar kanjamau ke yaduwa a cikin al’umma babu kama kafar yaro, kuma babu ruwanta da yaro ko babba, na kirki ko ja’iri, mace ko namiji, mai kudi ko talaka, da dai sauransu. A zauren mu na baki, mun tattauna da kwararren likitan tiyata na asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, kuma shugaban bangaren tiyata na sashen koyon aikin likita na Jami’ar Bayero ta Kano inda muka taba abubuwa da dama.

 

A daba’i na gaba idan Allah ya kaimu zamu ware wani sashe na musamman a wannan mujalla inda za’a baiwa mai karatu damar miko tambayoyi domin likitoci su duba kuma su bada amsa. Za’a iya yin tambayoyin akan cututtuka, hanyoyin rigakafi, harkokin aikin kiwon lafiya da jinya, da makamantansu.

 

Idan kaga wani abu da yake bukatar gyara a wannan mujalla, ko kuma kana da shawara, ko tambaya, koma kana bukatar tallan hajar ka ko manufar ka, maza hanzarta ka tuntubemu ta adireshin wannan mujalla. Haka kuma idan kana da wani rubutu/kasida/makala da kake so a saka a wannan mujalla, to duk dai ka aiko mana ta wannan adireshi. Sai dai idan kana so rubutun ka, tallan ka, ko tambayoyin ka su fito a daba’i na gaba, to ka aiko su kafin goma ga watan Agusta na shekera ta dubu biyu da shida miladiyya ko kuma goma ga watan Rajab na shekara ta alif da dari hudu da ashirin da bakwai bayan hijira).

 

Muna mika godiyar mu ga Iyayen mu, malaman mu, da kuma dukkan wadanda suka taimaka wajen kammaluwar wannan mujalla. Allah Ya saka da alkhairi.

 

Aminu Suleiman Jahun,

Babban Edita.

 

Mu tuna da cewa...

...An karbo daga Abu Huraira (RA), yace Mazon Allah (SAW) yace: “Kada ku yi hassada, kada ku yi algus, kada kuyi gaba, kada ku juya wa jununan ku baya, kada wani ya yi ciniki bisa cinikin dan’uwansa, ku zamo ‘yan uwan juna ya ku bayin Allah, musulmi dan uwan musulmi ne, kada ya zalunce shi, kada ya tabar da shi, kada ya wulaqanta shi, tsoron Allah yana nan (yana nuna qirjinsa, har sau uku). Mutum ya isa kai wa matuqa wajen sharri, ya wulaqanta dan’uwansa musulmi; ko wane  musulmi bisa dan uwansa musulmi, jininsa da dukiyarsa da mutuncinsa haramun ne.[Muslim ne ya fitar da shi – hadisi na 1525 cikin littafin Bulugul Maram littafi na biyu, na Al-Hafiz Alasqalani, fassarar Ibrahim Abubakar I. Tofa, shafi na 207.]

Yaduwar cutar kanjamau a cikin al'umma - Laifin wa?

...Duk da cewar bama ganin hakan a zahiri, ciwon qanjamau yana nan yana yaxuwa kamar wutar daji a tsakanin al’ummar mu, ba zamu gane hakan ba sai munje asibiti, inda za ka ga kusan kashi arba’in na marasa lafiyar da aka kwantar suna da wannan ciwo, in ka xebe wadanda ake kwantarwa don yi musu tiyata. Lallai ya kamata mu tambayi kanmu dalilin da yasa wannan irin annoba take yaduwa a tsakanin al’ummar musulmai, wadanda suke riko da littafin da daukacin duniya ta yarda da cewa shine littafi mafi cike da hikimomi, ilmin kimiyya da kuma na zamantakewa. Shin mun kasa gane yadda zamu magance wannan matsala ne a addinance, ko kuwa muna sane muka zauna cikin wannan bala’i wanda ke addabar kowa...

Zauren baki

A wannan daba’i, mun zanta ne da Dr. Sani Alhassan, kwararren likita kuma shugaban bangaren tiyata na sashen koyon aikin likita na Jami’ar Bayero ta Kano da Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dake nan Kano. Har’ila yau kuma shine shugaban kwamitin kula da kuma bada shawarwari (wato chairman – medical advisory committee) na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano...