Zauren Baki

Mujallar Lafiya Jari Laifin Wa? Zauren Baki Awon mata masu ciki Baiwar Allah: 'Yan tagwaye Cutar hawan jini Cutar sarke hakora Cutar tarin fuka Daula ta kwarai Gudawa Hattara Dai Iyaye Jan hankali akan Bola Makirce-makircen shaidan ZIKIRIN ALLAH

Tare da kwararren Likitan tiyata, Dakta Sani Alhassan (SA).

A wannan daba’i, mun zanta ne da kwararren likita kuma shugaban bangaren tiyata na sashen koyon aikin likita na Jami’ar Bayero ta Kano da Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dake nan Kano. Har’ila yau kuma shine shugaban kwamitin kula da kuma bada shawarwari (wato chairman – medical advisory committee) na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano. Hirar tamu ta kasance kamar haka –

LT –  Gafarta Malam, ko zaka bamu dan takaitaccen tarihin ka.

SA – Suna na Sani Alhassan. Na taso ne a wurin wani kawuna. Shi sunan sa Usman, kuma tunda yake a wurin sa na taso, kamar uba yake gareni, amma mahaifi na shine Alhassan. Na girma a unguwar Dakata a Kano daga 1968 zuwa 1973. Na je makarantar Federal Gobernment College ta garin Warri daga 1973 zuwa 1978. Daga nan na je School of Basic Studies a Zaria nayi karatu tsahon shekara guda. Bayan  na gama sai na je bangaren koyon aikin likita na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria a 1978, na kuma kammala har aka yaye mu a 1984. Daga nan na yi aikin sanin makamar-aiki (wato house job) a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello. Na kuma yi aikin bautar kasa bayan nan.

Na je kasar Ingila daga watan Augusta na 1988, zuwa watan Maris na 1997, watau kusan shekera goma kenan. Daga nan sai na komo sashen fida na bangaren koyon aikin likita na Jami’ar Bayero ta Kano. A wannan lokacin ba’a ba mu damar yaye sababbin likitoci kai tsaye ba (wato accreditation), amma yanzu Alhamdulillahi, wannan ya zama tsohon labari...

A yanzu ina aiki a wannan Jami’a a matsayin babban malami tun daga 1995 zuwa yau. Daga cikin wasu abubuwan da nayi sun hada da Bakon Malami Mai Kula Da Jarrabawa (edternal edaminer) ta likitoci masu neman kwarewa a tiyata da bangaren fitsari ta daya da ta biyu (part I and Part II).

LJ – Me ya ja hankalin ka har kayi sha’awar shiga aikin likitanci, kuma a ganin ka wadanne matsaloli aka fi fuskanta a wannan fanni na tiyata?

SA – … likitanci, na sami kaina ne aciki. Daga fari, naso in karanci aikin injiniya (wato engineering) a can kasar Canada, amma da na samu School of Basic Studies Zaria, sai na sauya ra’ayi na zuwa likitanci.

Babbar matsalar da ake yawan samu da mutane a wannan bangare na likitanci ita ce a da mutane na wahala idan anzo yin tiyata don haka suke tsoro. Amma yanzu abubuwa na canzawa. A kasashen waje harma ana da hanyoyi wadanda suke magance wannan tsoro. Kamar idan za’a yi wa yaro tiyata, sai a saka masa majigi (cartoon) yai ta kallo don ya dauke masa hankali, da sauran irin wannan.

Wata matsalar kuma ita ce yanzu idan ka duba, zaka ga wato mutanen da basu cancanta su bude wuraren kula da marasa lafiya ba sai su bude. Don haka idan mara lafiya ya je baza a kula da shi yadda ya kamata ba, daga nan kuma sai cutar ta kara tabarbarewa, ayi ta jeka-ka-dawo. Wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa wasu ke neman hanyoyin da suke ganin sun fi sauki, kamar magungunan gargajiya. Wato baza su zo asibiti da wuri ba sai sunje an gama lalata jikin, cuta kuma ta ci ta cinye tukun... Har ma ta kai wasu na cewa idan mutum yazo wannan asibitin baya fita.

LJ – Kana ganin za’a iya gwada wannan asibitin namu da takwarorin sa na kasashen waje da suka cigaba?

SA – A gaskiya ba za’a gwada wannan asibitin da na kasashen waje ba. A can an dauki wannan harka da muhimmanci. In ka dauki karamin asibiti zaka ga yana da kayan aiki isassu. A can doka bata yarda kaje waje domin magani ba, kuma gwamnati ta na bada muhimmanci wajen sayen magunguna masu kyau, da sauransu. Don haka ba za’a iya kwatanta wannan asibitin da na kasar waje ba. Ba mu da isassun kayan aiki, ga misali irin su na’urar hoton jijiyoyin jini (angiography machine) wanda yana kaiwa wajen naira million dari (100 million naira). A Najeria ma guda uku kawai ake da su. Amma za ka ga cewa duk in da ka je a turai, ko gari kamar Wudil, zaka samu suna da wannan na’ura.

Kuma suna bawa ma’aikatan su horo yadda ya kamata. Kuma duk inda aka sami wani sabon abu za’a tura su suje don su sami horo a kansa. Haka kuma likitocin mu da suka kware can suke tafiya. Idan kaje zaka ga mutanen mu da suka kware a fannin zuciya, koda da sauransu. Mutane na guduwa can ne saboda a can akwai kayan aiki so sai, ga kwanciyar hankali da tsaro, babu ruwan ka da ‘yan fashi, da sauransu.

LJ – To yaya kake ganin in an gwada namu asibitin da sauran asibitocin kasar nan?

SA – Jami’an hukumar kula da Jami’o’i ta kasa (wato National Unibersities Council – NUC) sun zo sun duba wannan asibitin sun kuma ce shine na biyu a kasar nan, misali wajen daukar ma’aikata, da kayan aiki ana kamantawa. Don haka daga asibitin koyarwa na Ibadan sai mu. Abubuwa da yawa da muke yi sauran asibitocin koyarwa basa yi. Kuma mun ci sa’a shugaban wannan asibitin na yanzu (Dr. A. I. Dutse) da wanda ya sauka (Dr. Wali) sun taimaka, sun yi kokari wajen daukan ma’aikata masu kishin aikin, da sauransu. Don haka a nan arewa dai babu kamar mu.

LJ – Kwanan baya an sami labarin wasu ‘yan biyu da suka fito a hade. Menene gaskiyar labarin, kuma dama hakan tana iya faruwa?

SA – Wadannan ‘yan biyu sun fito a hade. Maza ne duk su biyun. Wato sun hade ta cikinsu, azzakarinsu, kugunsu, hanji da kuma mararsu. A shekarar 1964 an taba haihuwar wasu wadanda su duk mata ne. Yanzu ma daya tana da rai har da ‘ya’yanta.

Su wadannan ‘yanbiyu maza haihuwar babar su ta goma kenan. A lokacin haihuwar tasu ta sami rauni a mahaifar ta wanda ya sa ta zubar da jini sosai don haka an kawo su wannan asibitin dakin yara.

Bayan sun kai iya girman da ake bukata kuma an tabbatar da sauran abubuwan da ake bukata, anyi musu tiyata, lokacin suna kwana ashirin da biyar. Daya daga cikin su kwayoyin cuta ne suka shiga jikin sa har ya rasu. Dayan kuma sai bayan kwana goma sha uku da yin tiyatar ya rasu. Shi wannan har yanzu bamu san dalilin rasuwar sa ba.

LJ – Gafarta malam, akwai wani jan hankali kuma da za ka yi wa mai karatu?

SA – Jan hankali anan, musamman ga dalibai masu koyon aikin likita shine muna bukatar likitoci. Idan kuka ci jarrabawar ku, kada kuma ku ce zaku gudu daga kasar. Don ko a kasar Ingila yanzu an daina bawa wanda ba dan kasa ba aiki sai dai idan ba’a sami dan kasan da zai iya ba. Domin sun kula ko ina baki ne suke yi musu aiki. Ranar da yaki ya taso mutane sa iya cewa gida za su tafi su taimakawa kasashen su. Don haka suka yi doka. Suna kokarin suma yaran su su taso. Yawancin kwararrun nasu baki ne ‘yan kasar India da Pakistan da kuma ‘yan Afrika, musamman ‘yan Najeria. Don haka muma ya kamata muyi kishin kasar mu. Muna da kwararru a fannin zuciya da koda da sauransu; da ace zasu dawo gida ai da ba haka ba.

Haka kuma mutane kar suce bini-bini sun tafi kasar waje domin neman magani. Misali gwamnatin Kano ta kashe wajen miliyan dari biyu (200 million) a tura mutane kasar waje neman magani, wanda da za’a iya amfani da shi wajen sayen na’urori daban daban wadanda zasu taimaka kwarai da gaske. Saboda haka ya kamata mutane su gyara.

LJ – Allah Ya gafarta, Mun Gode.

domin neman karin bayani, tuntubemu ta adireshinmu na email kamar haka: