Laifin Wa?

Mujallar Lafiya Jari Laifin Wa? Zauren Baki Awon mata masu ciki Baiwar Allah: 'Yan tagwaye Cutar hawan jini Cutar sarke hakora Cutar tarin fuka Daula ta kwarai Gudawa Hattara Dai Iyaye Jan hankali akan Bola Makirce-makircen shaidan ZIKIRIN ALLAH

Yaduwar cutar kanjamau a cikin al'umma - Laifin wa?

Misbahu Haruna Ahmad, 600L MBBS, BUK/AKTH, ahmadmisbahu@yahoo.com

“Haba A’isha, ke kin fiye dokin tsiya. Nan da wata daya ne fa za’a yi bikin, in yaso in ma in hadiye Zaharaddin din zaki yi sai ki yi”.

“Hmm ke ma dai Nafisatu kin san ina matuqar son sa wallahi”, A’isha tace.

A’isha yarinya ce mai hankali, addini, kamun kai, da sanin ya kamata. A yanzu tana da shekaru goma sha bakwai kuma ta gama karatun sakandire, har ma ana shirye-shiryen bikinta da wani saurayi mai hankali da addini irinta mai suna Zaharaddin wanda yake aiki a wani kamfani a jihar Kano. Duk da dai kafin a tsaida magana wani magidanci attajiri mai suna Alhaji Isa ya nemi auren A’isha, hakan bata cimma ruwa ba  kasancewar da aka bawa A’isha  zabi ta nuna hankalinta yafi kwanciya da Zaharaddin.

Shekaru biyu baya da suka wuce, Zaharaddin ya halacci wata bita ta sanin makamar aiki a Abuja tare da wata abokiyar aikinsa mai suna Monica. Abin tsautsayi da takaici cikin kwana uku da suka yi a hotel, sai da Monica ta sami nasara ta ribaci Zaharaddin har ta kai da ya santa ‘ya mace. Zaharaddin yayi matukar nadama da takaici daga baya, daga qarshe ya nemi  gafarar Ubangiji da niyyar ba zai sake bari hakan ta kuma faruwa ba.

Kafin Anti Saratu ta  koma kasar Iran, inda aka tura mijinta a matsayin Jakadan Najeria, ta yi matuqar qoqari ta shawo kan yayanta Alhaji Umar (mahaifin A’isha) ya yarda a yi gwajin jini kafin auren A’isha da Zaharaddin don gudun amosanin jini (sikila)  da sauran cututtuka na zamani kasancewar ita ma’aikaciyar jinya ce, amma hakan yaci tura saboda a ganin mahaifin A’isha yin hakan rashin yarda da ‘yarsa ne da kuma nuna rashin yarda da shi Zaharaddin din, wanda kowa a unguwar ya sanshi wajen kamun kai, addini da girmama na gaba. Ita kanta A’isha tafi yarda da ra’ayin mahaifin nata da kuma tunanin kar buqatar yin hakan ta batawa Zaharaddin rai. A qarshe dai da Anti  Saratu ta tsananta sai Alhaji Umar ya yanke shawarar neman fatawa wajen Sheikh Mustafa Ziri wanda wani sanannen malami ne a Kano. Sheikh Mustafa ba tare da wani bata lokaci ba ya bayar da fatawa cewa yin gwajin jini kafin aure koyi ne da yahudu da nasara wadanda Manzon Allah (SAW) ya umarce mu da mu saba musu a komai. Dadin dadawa ma yin haka kawo bidi’a ne da wani sharadi a cikin aure wanda manzon Allah bai yi ba kuma bai koyar da shi ba.

Shekara biyu bayan auren sai A’isha ta sami juna biyu inda tayi ta fama da laulayi da yawan masassara har saida aka kwantar da ita a asibiti. Bayan wata daya sai ta haifi ‘ya mace wacce saboda laulayin da A’isha tayi ta fama da shi bata zo da qoshin lafiya ba. Bugu da qari wannan lokaci shi kansa Zaharaddin yana ta fama da yawan zazzabi, tari da gudawa wadanda duk suka sa ya rame. Bayan ‘yan watanni sai Allah yayi masa rasuwa inda aka yi tsammani cutar TB ce ta kashe shi. Wannan al’amari ya girgiza A’isha qwarai har ya jawo qara tabarbarewar lafiyarta. Daga bisani yarinyar ma Allah yayi mata rasuwa, A’isha kuma ta sami sauqi. Sai dai Dr. Aliyu wanda shine likitan da yake kula da ita ya sanar mata da cewa ta kamu da cutar qanjamau, amma in har ta kwantar da hankalinta ta sha magani, to ba za’a a gane cewar ma tana dauke da ciwon ba. Hankalin A’isha yayi matuqar tashi, amma daga baya ta yanke shawarar ba zata  bari kowa ya san hakan ba, don kare  martabar marigayi Zaharaddin, ta kuma roqi Dr. Aliyu da kada ya sanar da mahaifanta ko ‘yan uwanta ya kuma yi mata alqawarin hakan sannan ta fara shan magani.

Bayan A’isha ta gama idda, sai ta fara koyarwa a wata makarantar firamare dake kusa da su. Amma bata jima ba sai tsohon maneminta Alhaji Isa ya sake nemanta da aure. Ba tare da wani bata lokaci ba sai mahaifinta ya bashi aurenta duk kuwa da matuqar nuna qin hakan da A’isha tayi, kasancewar ta kasa bada hujja mai qwari a kan niyya da tayi na cewa ba zata sake aure ba. A’isha ta shiga wani matsanancin hali har taje ta sanar da Dr. Aliyu, amma tsoron kallon da mutane zasu dinga yiwa A’isha da kuma tsohon mijinta sai ya hana su dauki wani mataki. Daga qarshe dai A’isha ta yanke shawarar ta mai da lamarinta ga Allah, tabi umarnin mahaifinta, ta kuma ja bakinta tayi kurum.

Bayan shekara daya da rabi da auren A’isha da Alhaji Isa sai Alhaji yaje wajan likitansa dan caje lafiyar jikinsa da yakan je ayi duk bayan shekara. Cikin matuqar juyayi likitan ya sanar da Alhaji Isa cewar yana dauke da qwayoyin  cutar qanjamau a jikinsa amma za’a sake yin gwajin da wasu sinadarai masu qarfi don tabbatar da hakan. Duk da haka hankalin Alhaji yayi matuqar tashi. Inda a sabili da tsunduma da yayi cikin tunani sai yayi hadarin mota a hanyarsa ta zuwa gida inda ko shurawa bai yiba. Kasancewa matan Alhaji Isa guda hudu sun gaji dukiya mai yawa bayan an raba gado, basu jima da gama idda ba sai wasu magidantan suka neme su da aure!…Kamar haka ne ciwon qanjamau yake yaduwa a wannan Al’umma ta mu cikin ruwan sanyi ba tare da mun sani, ko mun dauki wani mataki don kare afkuwar hakan ba.

Duk da cewar bama ganin hakan a zahiri, ciwon qanjamau yana nan yana yaduwa kamar wutar daji a tsakanin al’ummar mu, ba zamu gane hakan ba sai munje asibiti, inda za ka ga kusan kashi arba’in na marasa lafiyar da aka kwantar suna da wannan ciwo, in ka debe wadanda ake kwantarwa don yi musu tiyata. Lallai ya kamata mu tambayi kanmu dalilin da yasa wannan irin annoba take yaduwa a tsakanin al’ummar musulmai, wadanda suke riko da littafin da daukacin duniya ta yarda da cewa shine littafi mafi cike da hikimomi, ilmin kimiyya da kuma na zamantakewa. Shin mun kasa gane yadda zamu magance wannan matsala ne a addinance, ko kuwa muna sane muka zauna cikin wannan bala’i wanda ke addabar kowa, harma da mutane na gari da masu tsoron Allah? Shin har yanzu Allah bai ganar da mu yadda zamu magance wannan matsala bane ko kuwa mun sani muke take sanin?

Lallai akwai buqatar malaman wannan al’umma da masana kimiyyar likitanci su zauna su tattauna, su fahimci juna akan wannan annoba domin Allah madaukakin Sarki na yabon wadanda yake misaltawa da cewa

Wadanda suke amsa kiran Ubangijinsu, su ke tsaida Sallah kuma suke fuskantar duk abinda ya shafe su ta hanyar tattaunawa a tsakaninsu, kuma suke ciyarwa daga abinda muka arzuta su (Surar Shura aya ta 38).

Don haka ya kamata su hada kai su wayar da kan al’umma cewa ciwon kanjamau ba ciwo ne na fasikai da mazinata ba kawai. A’a, ya kan ma kama mutane nagari masu tsoron Allah da bin dokokinsa kamar Zaharaddin, A’isha da Alhaji Isa a cikin wannan labari. Kai harma da wanda bai jiba bai gani ba kamar jaririyar da A’isha ta haifa wacce ba ta ma san wani abu waishi sabo ba amma gashi ciwon ya kama ta tun tana ciki, ya kuma zama sanadi na salwantar rayuwarta tun kafin ta san me duniya take ciki. Bugu da qari wasu na iya kamuwa da ciwon ta hanyar qarin jini da ba’a tantance ba, ko kuma masu aikin asibiti wadanda zasu iya jin rauni da kayan aikin da jinin masu dauke da ciwon ya taba. Don haka kada mu rinqa qyamatar su ba dalili don kar qoqarin su tsira da mutuncinsu yasa su yada cutar ga wasu mutane daban, kamar yadda ya faru da A’isha.

Ya kamata kuma su warware matsalar yin gwaji kafin aure don tabbatar da  cewar shin yin hakan haram ne, halal ne, ko kuma ma wajibi ne, idan muka yi la’akari da halin da muke ciki yanzu da kuma la’akari da cututtukan da littafan mu na addini suka tabbatar da cewa suna hana qulluwar aure kamar su kuturta, da hauka, wadanda illar da suke kawo wa sam ba ta kama qafar  ta qanjamau ba. Mu kuma yi la’akari da cewar ciwon qanjamau ciwo ne da ke tabawa mutum hankalinsa, mutuncinsa, addininsa, da kuma dukiyarsa, wadanda suna cikin haqqoqi biyar da a kowane lokaci addinin musulunci yake karewa dan-adam su. Babu yadda za’ayi kuwa a kare wadannan haqqoqi na al’umma in har likita zai ce shi zai fadi hukuncin abubuwan da suka shafi wannan cuta a addinance, ko kuwa malami yace shi yafi kowa sanin wannan ciwo. Hakanan ma  yin hakan na iya kusanta mu da mutanen da Allah Madaukakin Sarki yake cewa:

Idan wani al’amari daga aminci ko tsoro (da ya shafi Al’umma) yaje musu sai gaggauta yada shi. Da kuwa sun mayar da shi zuwa ga Manzo da masu jibintar al’amura daga cikinsu, lalle da wadanda suke yin bincikensa zasu san shi. Kuma ba domin falalar Allah ba a kan ku da rahamarsa, hakika da kun bi Shaidan face kadan (daga cikin ku) (Surar Nisai, aya ta 83).

A qarshe ya kamata mu gane cewa, ba kowane abu bane dan yazo daga turawa yinsa zai zamanto koyi dasu, domin Manzon Allah (SAW) yana cewa “Ita kalma ta hikima wani abu ne na mumini da ya bata, ko ina ko ya ganshi, to shi yafi cancanta dashi” (Tirmidhi). Kuma muna sane da cewar Manzon Allah (SAW) yayi aiki da hikimar da mutanen Farisa suke yi ta haqa kadarko kewaye da gari don hana mahara shiga, duk kuwa da cewa mutanen Farisa a wannan lokacin mushirikai ne masu bauta wa wuta.

In har mun yarda yin gwaji kafin aure wajibi ne, to zai yi kyau gwamnatin mu da masu jibintar al’amuran mu su kafa wasu cibiyoyi da zasu dauki alhakin tabbatar da yin hakan. In kuwa muna ganin yin gwajin haramun ne, to ya zama wajibi mu qirqiro hanyoyi irin namu da zamu kare yaduwar wannan cuta cikin al’ummar mu. In kuwa ba haka ba to ta yiwu Allah ya kama likitoci, malamai da shugabanni na wannan al’umma da sakaci wajen kare haqqoqin na qasa da su. Allah yasa mu dace, ya kuma sa ilmin da ya bamu ya zamanto hujja garemu ta yin abinda ya kamata; ba ya zamo hujja a kanmu ba don rashin yin aiki da shi.

Dukkan abin da na fada dai-dai, to daga Allah ne, wanda kuma na fada kan kuskure to Allah ya gafarta min.

Domin neman karin bayani, tuntubemu ta adireshinmu na email kamar haka: